Kotu ta bayar da sammacin kama Alkalin alkalai Walter Onnoghen

Walter Onnoghen. Hakkin mallakar hoto @CREVO360_NG

Kotun da'ar ma'aikata (CCT) ta bayar da sammacin kama alkalin alkalan Najeriya da aka dakatar Walter Onnoghen.

Babban alkalin kotun ne mai sharia Dandali Umar ya bayar da sammacin kama Alkalin alkalan a ranar laraba.

Jami'in hulda da jama'a na kotun da'ar ma'aikatan Ibrahim al-Hassan wanda ya tabbatar wa da BBC da labarin, ya ce kotun ta amince ne da bukatar da masu gabatar da kara suka gabatar.

"Kotun ta amince da sammacin kama Alkalin alkalan bayan ya ki gurfana gabanta domin kare zargin da ake ma sa," in ji shi.

Ya ce alkalin kotun ya bayar da umurnin a kawo Onnoghen ranar juma'a 15 ga watan Fabrairu.

Ya kuma ce kotun ta umurci jami'an 'yan sanda da na farin kaya su kama shi bayan ya kauracewa zaman kotun a ranar Laraba.

Laifuka shida ake tuhumar Alkalin alkalan, dukkaninsu da suka shafi kin bayyana dukiyar da ya mallaka.

Sammacin kama shi kuma na zuwa ne bayan lauyoyin da ke kare shi sun kalubalanci kotun cewa ba ta karfin da za ta gurfanar da Alkalin alkalan da aka dakatar.

Batun zarginsa da kuma dakatar da shi sun janyo ce-ce-ku-ce a ciki da wajen Najeriya, inda manyan kasashen duniya suka bayyana damuwa kan tasirin dakatar da shi ga tabbatar da sahihin zabe a 2019 kamar yadda 'yan adawa suka yi korafi.

A watan Janairu ne shugaba Buhari ya dakatar Alkalin alkalan inda 'yan adawa kuma suka ce ba ya da karfin da zai dakatar da shi.