Motoci 300 sun bata bayan kammala wani taro na kasashen duniya

Five Maseratis seen at Port Moresby airport, draped in protective white covers Hakkin mallakar hoto AirBridgeCargo
Image caption An gano wasu motocin samfurin Maserati

'Yan sanda a kasar Papua New Guinea suna neman a dawo da kusan motoci 300, wadanda aka ara wa jami'an da suka halarci wani taron tattalin arziki na yankin Asia-Pacific a bara.

An sayi motocin ne domin a dinga zirga-zirga da shugabannin kasashen da suka halarci taron, a kasar da ke fama da talauci.

Amma wani babban dan sanda a ranar Talata ya ce 284 daga cikin motocin sun yi batan dabo.

Motocin sun hada da Landcruisers da Fords da Mazdas da kuma Pajeros, kamar yadda Superintendent Dennis Corcoran ya ce.

An girke wasu jami'ai na musamman a Port Moresby, babban birnin Papua New Guinea domin nemo motocin.

Superintendent Dennis Corcoran ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa: "Akwai motoci 284 da aka bayar don amfanin manyan jami'ai lokacin taron, amma har yanzu ba a dawo da su ba."

Ya kara da cewa an yi sa'ar gano motocin da suka fi tsada daga cikin motocin, wato Maseratis, wadanda kudinsu ya kai dala dubu 100.

"Dukkan motoci samfurin Maseratis 40 da kuma samfurin Bentley na cikin yanayi mai kyau, kuma an kulle su a wani waje na musamman," a cewarsa.

A cewar 'yan sanda, tara daga cikin motocin da suka bata din an sace su ne, an kuma cire wasu bangarori nasu. Yayin da sauran da aka gano kuma duk an musu illa.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption 'Yan kasar da dama sun yi ta sukar taron

Shugabannin kasashen yankin Pacific na Kudu mai al'umma miliyan 7.3 sun yi fatan cewa taron zai jawo hankalin masu zuba jari da kuma kasashen duniya cikin kasar.

Sai dai daukar nauyin taron ya sa tattalin arzikin kasar cikin wani yanayi, har sai da ta bukaci taimako daga wasu kasashen.

Australiya da Amurka da Zealand duk sun tura dakaru na musamman taron don tabbatar da cewa mahalartan na cikin aminci.

A lokaci guda kuma, kafafen yada labarai da masu fafutuka sun yi ta diga alamar tambaya kan ko ya dace matalauciyar kasa irin wannan ta dauki nauyin gagarumin taro irin haka.

Masu suka na ganin daruruwan motocin da aka saya din a matsayin almubazzaranci.

Labarai masu alaka

Karin bayani