Kaunar da Philip yake yi wa harkar gandun daji

The Duke on a tour of Cameroon and Gabon in 1999

Asalin hoton, Shutterstock

Namun Daji da kiwonsu wani fanni ne da Maimartaba Duke na Edinburgh yake sha'awa a rayuwarsa.

Ana shirya masa yawon shakatawa irin na gidan sarauta, don taimaka masa ya cika burinsa na sha'awar Gandun Daji, ciki har da ziyara a yankin Antartic wanda ya ba shi damar yin ido-hudu da namun daji.

Amma tun da farko ya san irin hadarin da wasu namun dajin ke da shi ga Dan'adam.

''Mutum ne mai sha'awar kiwon namun daji tun kafin kiwon ya shahara ko ma ya zama abin sha'awa a duniya.'' A cewar tsohon Shugaban Kungiyar Masu Kare namun daji ta Duniya, Charles Secrett.

''Muhimmin batun shi ne, ya sa mutane sun mai da hankali wajen sanin matsalolin da namun daji ke fuskanta, musaman ma na barazanar karar da su a doron kasa da kuma lalata musu muhalli.''

Yarima Philip ya zama kamar wani mutum da Allah ya hallito domin ya zama shugaban Gidauniyar Kula da Namun Daji ta Duniya, kamar yadda ake kiranta a wancan lokaci.

Ya yi amfani da kaunar da yake yi wa namun daji wajen cin nasarar manufofin kungiyar, kamar shirin ceton rayuwar dabbar nan da ake kira ''Panda''a Turance.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Duke da Tim Walker, shugaban WWF-UK na Jami'ar Landan 1986

A cewar Maimartaba Duke, kare rayuwar dabbobi irin Panda batu ne daraja nau'o'in halittu, ba wai kare rayuwar wata dabba guda daya ba.

Ya taba cewa''A gani na abin sha'awa ne matuka a ce akwai halittu daban-daban masu ban sha'awa a doron kasa, wadanda rayuwarsu ke amfanarmu sannan kuma tamu take amfanar su.''Ya kara da cewa ''Ina tsammanin da ace mu mutane muna da ikon kashewa da rayawa, ya kamata mu yi aiki da hankali wajen kisan da rayarwar.

Don haka mai zai sa mu karar da wasu dabbobi idan babu bukatar yin hakan.''

Farauta

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Ko da yake a da can akan kashe namun daji da sunan farauta. Wata rana sun fita rangadi shi da sarauniya sai ya harbi wata damisa har ta mutu. Daukar hoton damisar da aka yi a lokacin sai da ya haifar masa da matsala a Kungiyar kare halittun daji ta Duniya.

Damisa a yanzu na fuskantar hadarin karewa a doron kasa, amma a wancan lokaci ba haka abin yake ba. "Wannan batu na kisan damisa na daya daga cikin abin da Yarima Philip takaicin aikatawa a tarihin rayuwarsa" in ji Mr. Secrett. "Amma fa cikin shekarun 1960 Al'amura sun sauya."

Bayan shekarun 1960, farautar namun daji ta zama babban batu a Birtaniya, kuma an halattata a Ingila da Scotland da Wales.

A wancan lokaci Yarima Philip ya goyi bayan Kungiyar 'yan farauta, batun da ya haifar da bacin rai a zukatan masu rajin kare hakkin namun daji na duniya.

Ya fito fili ya kare ra'ayinsa, inda ya ce; A gani na ba laifi ba ne ga mafarauta su yi farautar dabbobin daji da suka tsufa, matukar an bar kanana da matasa domin su cigaba da hayayyafa, kmara dai manomi

ne ''Kana noma kana girbi, kuma kana tanadin iri don gobe.''

Amma a sauran batutuwan da suka shafi gandun daji, Yarima ya samu fahimtar juna tsakaninsa da kusan dukkanin asu fafutukar kare namun daji.

Asalin hoton, Shutterstock

Bayanan hoto,

A wancan lokaci Yarima Philip ya goyi bayan Kungiyar 'yan farauta, batun da ya haifar da bacin rai a zukatan masu rajin kare hakkin namun daji na duniya

Tun daga wannan lokaci ne makomar namun daji a duniya ta samu kariya, bayan da aka canjawa kungiyar suna zuwa Gidauniyar Kare Halittun Daji ta Duniya, wato WWF a takaice.

A halin yanzu, babban abin da aka sa a gaba shi ne, yadda gwamnatoci za su shiga cikin shirin, musamman ma kasashe masu tasowa, don su rattaba hannu akan yarjejeniyar cigaba mai dorewa.

''Idan komai ya tafi yadda ya kamata, ba laifi ba ne ace gwamnatoci su zo sub a da kudin gudanar da wannan aiki'' In ji Mai martaba Duke.

''Ina ganin dayawa daga cikinsu ba za su zo su tafi hakannan ba tare da sun bad a wani tallafi ba, musamman ma dai idan sun amince sun rattaba hannu akan yarjejeniyar da wuya su ce a'a.''

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sai dai kafin a fara shirin magance matsalolin, ya yi ritaya, bayan shekaru 20 da ya yi a matsayin shugaban Kungiyar

Halin da tekunan duniya ke ciki da kuma kamun kifi da ake yi wanda ya wuce ka'ida na daga cikin matsaloli na karshe a bangaren muhalli da Yarima yake son a magance su a karkashin wannan Gidauniya.

Sai dai kafin a fara shirin magance matsalolin, ya yi ritaya, bayan shekaru 20 da ya yi a matsayin shugaban Kungiyar.

Duk da cewa Yarima ya kai shekarunsa na yin ritaya daga kungiyar, an cigaba da damawa da shi a harkokin kungiyar, kuma ya cigaba da aiki kamar yadda aka san shi.

Asalin hoton, Alamy

Bayanan hoto,

Duke da dabbar Panda a lokacin wata ziyara da ya kai China a Oktobar 1986

Kamar yadda Mista Secrett ya ce'' Yarima yana fadin ra'ayinsa gaba-gadi, yana tsage gaskiya komai dacinta, akan abin day a yi imani gaskiya ne, ba tare da la'akari daw a yake sauraronsa ko kasaitar wanda yake Magana da shi ba, ko me sakamakon hakan zai haifar kuwa.''

''Ko da ba a samu fahimtar juna ba, babbar nasara ce ga mutum ya yi gamsasshen bayani akan gaskiya da adalci.''

Babban abin da Gidauniyar Kare Gandun Daji ta fi yin kewa game da rashin Yarima shi ne, dagewa da jajircewarsa akan dukkanin abin da ya sa a gaba.

Asalin hoton, PA