Prince Philip: Yadda Yarima ya ziyarci kasashe 143

Queen Elizabeth II and the Duke of Edinburgh disembarking from the Royal Yacht Britannia in Portsmouth dockyard on 29/06/1977

Asalin hoton, PA

A matsayinsa na basaraken Birtaniyan da ya fi dadewa a ayyukan agaji, Mai martaba Duke na Edimburgh ya shafe shekaru da dama yana raka sarauniya a rangadin da take yi zuwa kasashe rainon Ingila, da ma wasu kasashen na daban.

Sannan kuma shi a karan kansa Yarima Philip, ya yi tafiye-tafiye zuwa kasashen waje har sau 637. Daga cikin wannan adadi, tafiya 229 ya yi tane zuwa kasashe 67 na renon Ingila.

Sannan sauran tafiye-tafiye 408 ya yi su ne zuwa sauran kasashe.

Princess Elizabeth and Prince Philip, the Duke of Edinburgh, riding in the back of their car, with Canadian Air Force Equerry Wing Commander Cox (front), through the crowded streets of Quebec, 12 October 1951

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Duke da Gimbiya a wancan lokacin suna zagayawa a birnin Quebec a watan Oktobar 1951
Princess Elizabeth and the Duke of Edinburgh admiring the view from a bridge in the grounds of Sagana Lodge, a wedding present from the then colony of Kenya. 5 February 1952:

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yarima Philip da Gimbiya Elizabeth suna hutawa a Kenya lokacin da suka samu labarin rasuwar mahaifinta

Bayan rasuwar sarki George VI wanda hakan ya sa Gimbiya Elizabeth ta zama sarauniya, sun yi tafiya ita da angonta a shekarar 1952.

Daga nan ne Mai martaba Duke ya ci gaba da tafiye-tafiyensa na ziyarar aiki har zuwa kasashe 143.

Jim kadan da fara mulkin sarauniya, sai ma'auratan suka fara wata ziyara ta wata-shida zuwa kasashe renon Ingila, daga watan Nuwambar 1953 zuwa watan Mayun 1954, inda suka ziyarci kasashe 12 a mota, wasu a jirgin-ruwa, wasu kuma a jirgin sama.

Queen Elizabeth II (right) and the Duke of Edinburgh (second right) standing with the Mayor of Colombo, Mr T Rudra (centre), as the National Anthems are played, outside the Town Hall in Ceylon, April 10th 1954.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sarauniya da mijinta a Sri Lanka a watan Afrilun 1954

A shekarar 1956 Mai martaba Duke ya yi rangadi na wata-hudu da nufin fadada kasashe renon Ingila zuwa yankin Trans-Antarctic.

Tafiya ce ta bazata, don haka Birtaniya ce kasa ta farko da ta shiga yankin Antarctic, kuma Yarima ne basarake na farko da ya ratsa yankin.

Yarima ya fara yin tafiyar ne a jirgin ruwa da Mumbasa, inda ya yi tafiyar kimanin mil 40,000.

Ya bi ta kasar Seychelles da Ceylon, da Malaya, da New Guinea har ya isa Australia, inda a nan ne ya kaddamar da wasan Olympic na 1956 a birnin Melbourne na New Zealand da Antarctica da Tsibirin Falkland da Georgia ta Kudu da Tsibirin Gough da Tristan da Cunha da St Helena da Ascension da kuma kasar Gambiya.

Yarima ya rika daukar hotunan tsuntsaye a lokacin da yake tafiye-tafiye, kuma ya adana su da kyau, inda daga baya ya tattara su a cikin littafi guda daya da ya sanya wa suna ''Tsuntsaye daga Birtaniya ''wato '' Birds form Britannia'' a Turance. An kuma buga littafin a shekarar 1962.

Wani labari da aka buga a Mujallar Times a watan Yunin 1957, an jero hotunan wasu manyan namun daji cikin wasu hotuna dari da aka bajewa jama'a su kalla, a wajen taron bajekolin kayayyakin tarihi a matsayin tsarabar tafiyar Mai martaba Duke.

A taron bajekolin, har da hotuna guda 47 da wani Mista Edward Seago ya Zana, wanda ya hau jirgin ruwan Yarima a lokacin da yake tafiya zuwa kasar Australia.

Prince Philip presents a programme on his tour
Bayanan hoto, A watan Mayun 1957 Duke ya gabatar da wani shiri a BBC kan tafiye-tafiyensa na tsawon wata hudu a kasashen rainon Ingila a lokacin hunturun da ya gabata

A ranar kirsimeti ta shekarar 1956, maganganun da Yarima Philip ya yi a lokacin da yake tafiya a cikin jirgin ruwa, kuma ya aika da su Birtaniya, su aka fara sawa, kafin sarauniya ta yi wa al'ummar kasar jawabin murnar kirsimeti daga fadarta ta Sandringham dake Norfolk.

A cikin jawabin da sarauniya ta yi ta bayyana cewa; ''Muna zuba idon ganin lokacin da za mu sake kasancewa tare ni da mijina.''

Sai dai an yi cece-kuce a kan wannan tafiya ta Yarima.

Jaridun Birtaniya sun yi ta yin tambayoyi a kan tsawon lokaci da Yarima ya dauka a wajen rangadinsa, ba tare da amaryarsa ba.

Prince Charles (left) taking a picture as he visits the Acropolis with the Duke of Edinburgh (centre) and Princess Anne, Greece, September 16th 1964.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Duke da 'ya'yansa Yarima Charles da Gimbiya Anne a Acropolis na kasar Girka a 1964
Prince Philip, Duke of Edinburgh dressed as a caballero during a visit to Mexico, October 1964.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Duke a lokacin wata ziyara a kasar Mexico a watan Oktobar 1964

A lokacin da yake daf da kammala rangadin, sarauniya ta hau jirgin sama domin ta je ta hadu da mijinta a kasar Portugal, kwanaki biyu kafin ya fara rangadi a kasar.

A lokacin bikinsu na cika shekaru 25 da aure, a shekarar 1977, Sarauniya da Mijinta Yarima Philip sun yi wata tafiya zuwa kasashe rainon Ingila, sun ziyarci birnin Papua na New Guinea da birnin West Indies.

A gida Birtaniya kuwa, Sarauniya da Yarima sun ziyarci larduna guda 36 a fadin kasar, duk a cikin shekararsu ta bikin cika shekaru 25 da aure.

A shekarar 1979, ma'auratan sun shiga kasashen yankin Gulf a jirgin ruwa, inda suka ziyarci kasashen Kuwaiti da Bahrain da Saudiyya da Qatar da Tarayyar Daular Larabawa da kuma Oman.

Shekaru uku bayan nan kuma suka yi tafiya zuwa yankin Pacific ta Kudu.

Queen Elizabeth II and the Duke of Edinburgh - Her Majesty taking a photograph during their visit to Tuvalu

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Sarauniya a lokacin da take shekara 56 tana daukar mijinta a hoto lokacin da suka kai ziyara Tuvalu a 1982
Queen Elizabeth II and the Duke of Edinburgh with India's Prime Minister Indira Gandhi during Royal visit to India 1983

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Sarauniya Elizabeth II da mijinta Duke na Edinburgh da Firai Minista Indira Gandhi a Delhi, 1983
The Duke of Edinburgh pats an elephant, India, 1983 20/11/1983

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Yarima Philip ya ga giwa lokacin ziyararsa a dajin Kahna a Indiya

Yarima Philip ya ziyarci India sau uku. Daya daga cikin daukakar da Birtaniya ke da ita, ita ce ta samun 'yancinta da ta yi tun kafin sarauniya Elizabeth ta hau gadon mulki.

Mai martaba Duke ya fuskanci suka a shekarar 1997, bayan kasancewarsa Shugaban Kungiyar Kare Namun Daji na Farko da ya fara kashe zaki a kasar.

Ma'auratan sun kai ziyarar karshe zuwa kasar India a shekarar 1997, lokacin bikin cikarsu shekaru 50 da samun 'yancin kasar Indian.

Sai dai tafiyar ba ta yi dadi ba saboda kalaman da Sakataren Harkokin Birtaniya, Rabin Cook ya taba yi a kan yankin Kashmir, wanda hakan ya sa Firaministan kasar India ya bayyana Birtaniya a matsayin kasa ''mai Katsa-landan a harkokin wasu kasashe.''

Sarauniya ba ta taba ziyartar Isra'ila ba, amma a shekarar 1994 Yarima Philip ya zama Babban Basarake daga Birtaniya da ya fara ziyartar kasar.

Ya yi ziyara kasashe da dama na duniya ba tare da sarauniya ba, mafi yawan tafiye-tafiyen ya yi su ne lokacin da yake Shugabantar Kungiyar Kare Namun Daji, sai kuma tafiye-tafiye da ya rika yi a matsayin wakilin sarauniya domin halartar jana'izar manyan mutane a sassa daban-daban na duniya.

Prince Philip, Duke of Edinburgh, bursts out in laughter during a conversation with WWII veterans after a wreath-laying ceremony at the main Commonwealth war graves cemetery in Ramle on 30 October, 1994.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Duke ya gana da tsoffin sojojin da suka yi yakin duniya na biyu a Isra'ila a shekarar 1994
Former South African president Nelson Mandela (L) chats with the Duke of Edinburgh, Prince Philip at Drakenstein Prison, Paarl about 50 kms outside of Cape Town 05 November 2000. The two men attended an awards ceremony for juvenile prisoners held under the auspices of the International Awards Association, a development programme for young people.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yarima Philip na hira da tsohon shugaban Afirka Ta Kudu Nelson Mandela a kusa da birnin Cape Town a Nuwambar shekarar 2000

Ita ma Sarauniya ta yi tafiye-tafiye da dama bisa amincewar ofishin Kula da Harkokin Kasashen Waje, hakan ya kara nuna irin kakkyawar dangantaka ta Diplomasiyya tsakaninta da sauran kasashen duniya.

Kasashe uku ne kadai Sarauniya ta taba zuwa tare da mijinta a yankin Latin Amurka, inda suka ziyarci Brazil da Chile da Mexico.

Sai dai kuma shi Yarima Philip ya ziyarci kasar Argentina a 1962. Kuma rahotanni a wancan lokaci sun ruwaito cewa, shugaban kasar yana fuskantar bore, amma duk da haka ba a bari boren ya shafi karramar da aka shirya yi wa Mai martaba Duke ba.

Queen Elizabeth II (2nd R), her husband Prince Philip The Duke of Edinburgh, and their representative in Australia Governor-General Peter Hollingworth (L) meet aboriginal dancers from the Paitya Dance Group during a ceremonial welcome to mark the beginning of the Royal visit to Australia, February 27, 2002 in Adelaide.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sarauniya da mijinta sun gana da wasu masu rawar gargajiya a Adelaide a 2002
ABUJA, NIGERIA: Nigerian President Olusegun Obasanjo (L) toasts with Prince Philip, Duke of Edinburgh, during a reception in honour of Britain's Queen Elizabeth II at the State House in Abuja, Nigeria, 03 December 2003. Queen Elizabeth II arrived in Nigeria 03 December two days ahead of the Commonwealth summit, on her first state visit since the country won its independence from her rule in 1956.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo da yarima Philip yayin wata ziyararsa Najeriya a 2003

A shekara ta 2002, lokacin bikin cika shekaru 50 na sarauniya a kan karagar mulki, Sarauniya da mai gidanta sun yi tafiyar kimanin mil 40,000 a fadin Birtaniya da wasu kasashen duniya, ciki har da Jamaica da New Zealand, inda a nan ne suka fara haduwa ido-da-ido da dan-majalisa na farko maza-mata a duniya.

A yayin tafiyar tasu dai, lokacin da suka isa Canada, sun ya da zango, inda har suka shiga cikin wasan kwallon gora da ake yi a cikin kankara, kuma a nan suka hadu da mutumin da ya zama zakara a gasar hawa tsauni ta duniya, wato Mista Bryan Adams.

The duke watches orphans perform a fashion show in Kampala, Uganda in 2007

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Duke na kallon wasa daga yaran da mahaifansu suka mutu sakamakon cutar Aids a Kampala na Uganda a 2007
Queen Elizabeth II and Prince Philip, Duke of Edinburgh attend Halifax Common on June 28, 2010 in Halifax, Canada

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sun ziyarci Canada a 2010

Tun a cikin tafiye-tafiyen da suka yi na farko suka ziyarci kasar Australia a shekarar 1954.

Kuma sun koma kasar tare da wasu 'yan gidan sarautar Ingilan a tsakanin shekaru 60, bayan ziyararsu ta farko.

A shekarar 2006 sarauniya ta bude gasar wasanni ta kasashe renon Ingila, kuma daya daga cikin tafiyar da suka yi ta baya-bayan nan ita ce ta halartar taron shugabannin kasashe renon Ingila.

Queen Elizabeth II and Prince Philip, Duke of Edinburgh meet dignitaries as they visit Al-Alam Palace on 26 November, 2010 in Muscat, Oman

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yarima Philip da Sarauniya a Oman a Nuwambar 2010
Queen Elizabeth II, Prince Philip, Duke of Edinburgh (L), the Sultan of Oman, His Majesty Sultan Qaboos bin Said and British Foreign Secretary of State, William Hague (R) sit as they watch an equestrian event and horse racing, at the Royal Horse Racing Club ON nOVEMBER 27, 2010 in Seeb Oman. The Queen and Duke of Edinburgh formally began the second leg of her Gulf state visit yesterday.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sarkin Oman, Mai Martaba Sarki Qaboos bin Said, ya kalli wani wasan gargajiya tare da Sarauniya da mijinta

A shekara ta 2015, Sarauniya da mai gidanta sun ziyarci Tsibirin Malta a rangadinsu na kwana uku a tsibirin da dama can sun taba zama a cikinsa.

Sun hau kwale-kwale ne in da suka ratsa ta yankin Valletta wanda nan ne wurin da Sarki George VI ya yi sansani a shekarar 1943 domin nuna girmamawa ga tsofaffin 'yan mazan jiya na Birtaniya bisa jajircewarsu a kan abokan gaba a Yakin Duniya na Biyu.

Kuma da can sarauniya da mai gidan nata sun taba zama a yankin na Valletta lokacin farkon aurensu, daga shekarar 1949-1951 tun kafin sarauniya ta hau gadon mulki, sannan kuma shi ma Yarima Philip ya taba zama a yankin a matsayin sojan ruwa.

A shekara ta 2007, sarauniya da mai gidanta sun koma Tsibirin Mediterranean domin bikin murnar cikarsu shekaru 60 da aure.

Queen Elizabeth II and Prince Philip, Duke of Edinburgh after looking at the view from the Kalkara heritage site in Valletta Harbour on November 28, 2015 in Valletta, Malta. Queen Elizabeth II, The Duke of Edinburgh, Prince Charles, Prince of Wales and Camilla, Duchess of Cornwall are in Malta on the final day of a visit to the island that has been hosting the Commonwealth Heads of State Summit.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sarauniya da mijinta a Malta a 2015

Bayan shekaru masu yawa na tafiye-tafiye da Yarima Duke ya yi a duniya ya fahimci irin cigaba da wannan duniya ta samu ta fuskar fasaha.

Ya tabe cewa a shekara ta 2002 ''Duk mutumin da ya yi tafiye-tafiye irin wadanda muka yi zai yaba da cigaban da aka samu ta fuskar kera jirgin sama na alfarma kuma mai saukin kara, musamman ma idan ba bangaren fasinja gama-gari ka shiga ba, inda karar da ake ji ta fi yawa.''

Dukkan hotunan hakkin mallakar Getty Images da Press Association ne