Mene ne bambancin dage zaben Jega da na Mahmud Yakubu?

Mahmud Yakubu Hakkin mallakar hoto Getty Images

A yayin da hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta daga zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki sa'o'i kadan gabanin a fara kada kuri'a, mutane suna ta bayyana ra'ayoyinsu kan hakan.

Ana iya cewa an samu rarrabuwar kawuna wajen bayyana irin yadda kowa ke kallon lamarin.

Hukumar INEC bayar da hujjar cewa rashin isar kayan zabe a kan lokaci wasu wuraren ne ya sa ta daga.

Yayin da wasu ke cewa ai ba kan shugaban INEC Farfesa Mahmud Yakubu aka fara irin wannan abu ba tsohon shugaban hukumar ma Farfesa Attahiru Jega ya taba yi a 2015, wasu kuwa cewa suke yi ai wancan ya sha bamban da wannan karon.

Wannan dai shi ne karo na uku da aka taba daga zaben Najeriya.

A 2011 shugaban INEC Farfesa Attahitu Jega ya dage zaben kasar bayan da mutane har sun kafa layuka, a wasu wuraren ma an fara kada kuria'a.

A don haka ne BBC ta yi nazari kan bambancin da ke tsakanin daga zabukan biyu.

Waiwaye

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Farfesa Attahiru Jega ne ya soma dage zaben Najeriya

A ranar 8 ga watan Fabrairun shekarar 2015 ne shugaban INEC na wancan lokacin Farfesa Attahiru Jega ya dage manyan zabukan kasar, a lokacin da ya rage saura kwana shida a gudanar da su inda ya mayar da sabuwar ranar 28 ga watan Maris.

Farfesan ya sanar da dage zaben wanda aka sanya za a yi a ranar 14 ga watan Fabrairu, zuwa makonni shida.

Farfesa Jega ya ce ya yi hakan ne saboda barazanar matsalar tsaro da ake fuskanta.

A wancan lokacin ana tsaka da matsalar rikicin Boko Haram a arewa maso gabas, don haka ne hukumomin tsaron kasar suka ce rashin isassun dakarun da za su kare masu kada kuri'a a wannan yanki, na daga cikin dalilan dage zaben.


Me Jonathan ya ce?

A wancan lokacin, Shugaba Goodluck Jonathan ya nuna goyon bayansa ga shugaban hukumar zaben kasar, Farfesa Jega, bayan matsalar da aka samu ta dage zabe.

A hirar da ya yi da sashen Turanci na BBC, Shugaba Jonathan ya yi magana a karon farko a kan ce-ce ku-cen da ya biyo bayan dage zaben inda ya ce duk da yake bai ji dadin abin da ya faru ba, amma yana da kwarin guiwar cewa Farfesa Jega zai iya sauke nauyin da ke kansa na shirya zabe ingantacce a kasar.

Shugaba Jonathan ya bukaci jama'a su ci gaba da nuna hakuri da juriya, su kuma fito domin yin zaben a sabuwar ranar da aka sanya.

'Yan Najeriya dai sun harzuka matuka a wancan lokacin kan wannan al'amari.

Wasu da yawa sun yi ta zargin cewa gwamnatin Jonathan na son yin magudi ne shi yasa ta hada baki da Jega don dage ranar.

Daga baya dai mutane sun sanyawa zukatansu hakuri.


Dage zabe a lokacin Buhari

A lokacin da ya rage sa'a biyar a tafi layin zabe ne shugaban INEC Farfesa Yakubu ya sanar da cewa an dage zaben da mako guda.

Wannan sanarwa ta zo wa 'yan Najeriya a ba zata, domin kusan a iya cewa kowa a shirye yake tsaf don fita zaben.

A yanzu sabuwar ranar zaben ta koma 23 ga watan Fabrairun 2019.

Farfesa Yakubu ya ce an dage zaben ne saboda "wasu matsaloli da suka taso dangane da shirye-shiryen zabe, musamman jigilar kayan zabe ta hanyar da za a bude rumfunan zabe a kasa bai daya daga karfe takwas na safe ranar Asabar.

Bisa wannan dalili ne hukumar zabe ta yi taro ta dage zaben zuwa 23 ga watan Fabrairu.

Me Buhari ya ce?

Har yanzu Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari bai ce komai ba tukun, amma ofishin yaki neman zabensa ya yi Allawadai da matakin hukumar zaben kasar, INEC, na dage manyan zabuka.

Sanarwar da Mr Festus Keyamo, mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben ya fitar ta zargi INEC da hada baki da jam'iyyar hamayya ta PDP domin magudin zabe.

"Muna fatan INEC za ta zama 'yar ba-ruwanmu a annan harka ta zabe domin kuwa jita-jitar da ake watsawa na cewa an dage zaben ne da hada bakin babbar jam'iyyar hamayya ta PDP, wacce da ma bata shirya shiga zaben ba," in ji Mr Keyamo.

Martanin PDP

Tsoron kaye ne ya sa gwamnatin Buhari ta dage zabe —Atiku

Dan takarar shugaban Najeriya na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin Muhammadu Buhari da kitsa dage zaben kasar da zummar harzuka 'yan Najeriya.

Sai dai sanarwar da Atiku Abubakar ya fitar ranar Asabar ta yi kira ga 'yan kasa da kada su karaya wajen sake fitowa su kada kudi'unsu.

"Sun sani cewa 'yan Najeriya sun yi shirin kayar da su, shi ya sa suka rude suna yin duk abin da za su iya wajen ganin basu sha kaye ba," in ji tsohon mataimakin shugaban kasar.

Ya kara da cewa gwamnatin Buhari ta kwashe shekara hudu tana shirin zabe amma sai da aka zo gargara take neman kwancewa 'yan Najeriya zane a kasuwa.


Kun san tasirin dage zaben Najeriya?

Abokin aikinmu Naziru Mika'il ya rubuta mana sharhi kan irin tasirin da dage zaben Najeriya zai yi. A sha karatu lafiya:

Sanarwar hukumar zaben ta kada zukatan 'yan kasar da dama, kuma za ta jawo ce-ce-ku-ce musamman tsakanin manyan jam'iyyun kasar, domin babu shakka kalaman na Farfesa Yakubu ba za su gamsar da dama daga cikin 'yan Najeriya ba.

Wani abu da zai kara bakantawa mutane rai shi ne yadda hukumar ta shafe shekara hudu tana shirya wannan zabe, amma kwatsam sai a mintinan karshe ta sauya matsaya.

Gabanin zaben dai gobara ta tashi a wasu ofisoshin hukumar amma ta dage cewa hakan ba zai shafi shirnta na zabe, kuma a yanzu ba ta ambaci hakan a matsayin dalili ba.

Sai dai tambayar a nan ita ce, mai ya sa sai yanzu, mai ya hana hukumar fitowa ta bayyana matsayinta tun farko, kuma mai ya sa ba ta dauki darasi daga ayyukanta na baya ba.

Jama'a da dama sun kashe kudade, wasu sun bar ayyukansu, wasu sun yi doguwar tafiya domin zuwa wuraren da za su kada kuri'unsu. Wannan mataki zai bakanta musu rai.

Wasu na hasashen wannan dagewar ka iya shafar adadin mutanen da za su fito domin kada kuri'unsu a mako mai zuwa.