Abubuwa 5 game da dage zaben Najeriya

Zaben 2019 Hakkin mallakar hoto ECOWAS

A ranar Asabar 16 ga watan Fabrairun 2019 ne hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya ta shirya gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar tarayya a kasar.

Tun kafin karatowar zabe a kasar, hukumar zaben daidai da rana daya bata taba nuna cewa akwai matsala ko kuma tana fuskantar cikas ko tasgaro wajen samar da kayyayakin zaben ba.

Kwatsam sa'o'i kalilan kafin zaben, sai hukumar ta bayyana gazawarta a fili inda ta ce ba za ta samu damar gudanar da zaben ba saboda wasu matsaloli da suka sha karfinta.

Tun bayan haka, an ta yi samun ce-ce-kuce daga jama'a da jam'iyyun siyasa da 'yan kasashen ketare dangane da wannan batu.

Ga abubuwa biyar game da daga wannan zabe na Najeriya.


Hasara ga kasa da jama'ar kasa

Najeriya ta kashe makudan kudade wajen shirye-shiryen zabe musamman a jajibirin zabe da ya hada da kashe kudi wajen safarar kayan zabe, kudin biyan jami'an tsaro da jami'an zabe.

'Yan kasar da dama sun kashe kudade domin tafiya sassa daban-daban na kasar domin jefa kuri'a, 'yan kasuwa sun tsayar da kasuwancinsu haka ma'aikata sun bar wuraren aikinsu.

Daga zaben zai jawo hasara garesu domin kudaden da suka kasafta domin amfani da su kan iya samun gibi, domin kuwa duk wanda a cikinsu zai koma gida ya kara dawowa sai ya kashe wasu kudin.

Sanna akwai manyan hukumomi na kasashen waje da na cikin gida da suka kashe miliyoyin daloli wajen shirya wa wannan zabe, tare da shigowa cikin kasar daga wasu kasashen. Amma duk a iya cewa duk sun tashi a tutar babu.


Zubar da mutuncin Najeriya a idon duniya

Najeriya ce kasar da ake yi wa kirari da Giwar Afirka kuma mafi karfin tattalin arziki a nahiyar.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kasashe da dama sun zuba ido su ga yadda wannan zaben zai kasance, amma kash!! Sai aka ji cewa an dage wannan zaben.

Hakan zai iya janyo zubar da mutuncin kasar a idon duniya inda kasashe da dama za su ga kamar kasar ba ta mayar da hankali wajen ci gaban al'ummar kasarta ba.

Nuna gazawar hukumar zabe

Hukumar zabe mai zaman kanta a kasar ta shafe sama da kwanaki 1400 tana shiye-shiryen zabe a kasar.

Tun bayan da majalisar kasar ta amince da makudan kudaden da hukumar zaben za ta yi amfani da su wajen gudanar da zaben, babu wata alama ta matsala ko kuma nuna gazawa da hukumar ta nuna dangane da gudanar da zaben.

Babbar tambaya a nan ita ce me yasa sai a sa'o'in karshe hukumar za ta nuna gazawarta a fili na kin gudanar da zaben?

Masu fashin baki da dama a kasar na ganin cewa irin hujjojin da hukumar zaben ta bayar ba wasu hujjoji ba ne da za su iya gamsar da masu zabe a kasar.


Sanyaya gwiwar masu zabe

Zukata da dama na masu zabe a kasar sun karaya, gwiwowin su sun sanyaya, jikkunansu sun mutu haka ransu ya baci dangane da wannan lamari.

Wasu daga cikin masu zabe a kasar sun bayyana cewa za su koma garuruwansu kuma ba za su sake dawowa jefa kuri'a ba bayan doguwar tafiyar da suka sha ba biyan bukata.

Wasu kuma sun bayyana cewa suna nan daram-dam za su yi zabe amma sun fara nuna kokwanto a kan ko hukumar zaben za ta yi adalci dangane da wannan zabe?


Tasgaro ka kasafin kudin jam'iyyu

Jam'iyyu da dama tuni suka biya jami'ansu a sassa daban-daban na kasar domin sa ido da kula da rumfunan zabe a fadin kasar.

Haka a ranar zabe akwai kudade na musamman da jam'iyyu kan ware domin gudanar da wasu hidimomi da suka shafeta a ranar zaben.

Sakamakon daga wannan zaben, ya zama dole ga jam'iyyu su kara fitar da wasu kudade domin biyan wasu daga cikin wakilansu da suka tura sassa daban-daban na kasar.

Hakkin mallakar hoto ECOWAS