Boko Haram ta kashe mutum 11 a Maiduguri

'Yan sanadan kwantar da tarzoma a Najeriya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan sanda a Maidugurin jihar Borno sun ce an kashe mutum 11 tare da jikkata mutum 15

'Yan sanda a birnin Maiduguri na jihar Borno a Najeriya sun bayyana cewa kungiyar Boko Haram ta hallaka mutane 11 da kuma raunata wasu 15.

Wani shugaban kungiyar mayakan sa-kai ya bayyana cewa an kai harin ne da nufin dakatar da mutane zuwa rumfunan zabe.

Harin ya faru ne da safiyar Asabar a kudancin birnin, inda mayakan suka bude wuta, wasu 'yan kunar bakin-wake kuma suka tarwatsa kansu da bama-bamai.

A yau ne aka shirya gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin kasar, sai dai an dage zaben zuwa mako mai zuwa sa'o'i kadan kafin a fara kada kuri'a.

Aikace-aikacen 'yan ta'adda ya tilasta wa mutane da dama barin muhallansu a Borno, al'amarin da ya jawo hukumar zabe ta kirkiri rumfunan zabe a sansanonin 'yan gudn hijira.

Ko a ranar Laraba da ta gabata 'yan Boko Haram sun far wa ayarin motocin gwamnan Borno, inda suka kashe mutum uku.

Labarai masu alaka