Me ya sa INEC ke son a ci gaba da yakin neman zabe?

Bayanan bidiyo,

Dalilin da ya sa aka daga zaben shugaban kasa a Najeriya

Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta, INEC, ta bukaci 'yan siyasa su ci gaba da yakin neman zabe.

Wata sanarwa da kwamishin watsa labarai na INEC, Festus Okoye, ya ce sun dauki matakin ne domin bai wa 'yan siyasa damar sake tallata kansu sakamakon dage zaben da aka yi ranar Juma'a.

"Kafofin watsa labarai za su iya wallafawa da kuma watsa sakonnin 'yan siyasa har zuwa tsakar daren Alhamis, 21 ga watan Fabrairun 2019. Muna kira ga 'yan siyasa su yi biyayya ga dokokin zabe," in ji Mr Okoye.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce sun dage zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin tarayya daga ranar 16 ga watan Fabraitru zuwa ranar 23 ga watan Fabrairu.

Ya kara da cewa an dage zaben gwamnoni daga ranar biyu ga watan Maris zuwa ranar tara ga watan na Maris.

Farfesa Yakubu ya ce sun dauki matakin ne sakamakon matsalolin rashin kai kayan zabe a wasu yankunan kasar a kan lokaci.

Da ma dai 'yan kasar sun soki hukumar zaben bisa dage shi, suna masu cewa bai kamata ta bayar da wani uzurin dage shi ba tun da shekara hudu ta yi tana shiri.

Su ma 'yan siyasa - irinsu su shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomhole da Sanata Rabi'u Kwankwaso na jam'iyyar PDP, sun ce ba za su fasa yakin neman zabe ba tun da INEC ta dage shi.

Sai dai hukumar ta ce ba da gangan ta dauki matakin ba, tana mai cewa da muguwar rawa gwara kin tashi.

Gabanin dage zaben, harkokin Najeriya sun tsaya cak inda aka rufe kan iyakokinta da kasuwanni da filayen jirgin sama da na kasa da dai sauransu.

Masana tattalin arziki sun ce dage zaben zai yi mummunan tasiri kan tattalin arzikin Najeriya, suna masu cewa a cikin kwana daya kacal, Najeriya ta yi asarar akalla $1bn.

Asalin hoton, Getty Images