Zaben 2019: 'Yan Najeriya na yin kwalliya da jam'iyyu

Woman smiling with her arms wide
Presentational white space

Zabe a Najeriya na zuwa da yayi- a kan sauya salon shiga kuma teloli na yin ciniki a lokacin da ake kirkirar dinke-dinke masu jigo na siyasa.

Arike Adesida (wadda hotonta ke sama) na sanye da rigar da wani tela ya dinka mata don zuwa gangamin yakin neman zabe a Legas kuma ta ce tana so Shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC ya lashe zaben a karo na biyu.

Taron mutane masu karsashi, sanye da kaya masu launi na jan hankali suna halartar taruka don zuwan Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP kuma babban abokin hamayyar Buhari.

Woman wearing a hat that says Atiku Babes
Presentational white space

Kemi Raji na cikin wata kungiyar mata da ke kiran kanta "'Yan matan Atiku", sun ce: "Muna kaunar Atiku. Mun san cewa zai kawo sauyi a rayuwarmu da ta 'ya'yanmu."

Group of women wearing green and blue attire
Presentational white space

Mambobin wata kungiyar mata 'yan kasuwa sun fito don nuna goyon baya ga Buhari da dan takarar gwamna a jihar Legas a jam'iyyar APC.

Shugabarsu, Alaja Cif MA Adebunmi, sanye da riga mai launun shudi, ta ce shugaba ne mai son kawo sauyi" wanda yake da "rikon gaskiya".

"Ya yi wa mata 'yan kasuwa abubuwa da yawa. Sun ba mu bashi, wanda har mun biya kuma mun samu wasu kudaden."

Group of women
Presentational white space

Asusun lamuni na duniya ya yi kiyasin cewa tattalin arzikin da ba a tsare yake ba, ciki har da kasuwanni, sun hada kashi 65 cikin dari na kudin da ake samu a matsayin ladan aiki a Najeriya.

Wasu mata daga wata kungiyar mata 'yan kasuwa sun fito don nuna goyon baya ga Atiku Abubakar.

Short presentational grey line

Jagorarsu Hadiza Mohammed ta ce ba su amfana da tallafin da gwamnatin Buhari take bayar wa ba wanda aka yi wa lakabi da "TraderMoni"

Lokacin da jami'ai suka shiga kasuwar sun ba da tallafi ne ga "mutum biyu ko uku ba, ba kowa ba ne aka taimaka, a cewarta.

Woman wearing PDP clothes
Presentational white space

Taiwo Kalejaiye ta yi tattaki daga jihar Ogun zuwa Legas don halartar taron yakin neman zaben PDP, inda ta daura gwaggwaro mai launin kore, kalolin alamar jam'iyyar.

"Mutanen Buhari ba sa kaunar Najeriya, kansu kawai suke so," ta ce.

Man wearing ADP clothes
Presentational white space

Tajudeen Akanji, wani babban dan jam'iyyar APC ne a Kudu maso yammacin kasar, yana sanye da hular yarabawa wadda ake kira "abeti aja".

"I believe in the positive things that this president is doing. I hope he can continue to get rid of the decadence of the past," he says. da yi mana gyaran abubuwan da aka bata a baya," a cewarsa.

Man with APC body paint
Presentational white space

Alhaji Dauda, wanda ya kwashe sa'a guda yana shafe jikinsa da fenti a kalolin jam'iyyar APC ya ce: "Babu wanda ya biya ni in yi wanna, kawai ina kaunar Buhari ne."

man dressed in carnival costume
Presentational white space

Ayomide Fashina, wanda ya zo taron PDP da tawagarsa ta 'yan rawa domin nishadantar da mutane, ya ce: "Ba na goyon bayan Buhari. Mun wahala tsawon shekara hudu kuma ba ma so mu kara shan wata wahalar."

PDP material in close up
Presentational white space

Hajiya Pine Olapade, wadda ta zo daga kudu maso gabashin kasar sanye da wani zani mai kwalliyar duwatsu da surfani na mutanen jihar Rivers ta ce: Atiku ne kawai zai iya farfado mana da tattalin arzikinmu. 'Yan Najeriya sun gaji. Muna son ganin sauyi."

Man selling APC hats
Presentational white space

An kawo kayan sayarwa da yawa wurin taron. Olumide Olumide ya je taron APC yana fatan samun kudi, amma kuma yana goyon bayan jam'iyyar.

"Shugaba Buhari mutumin kirki ne. A lokacin mulkin Goodluck Jonathan akwai cin hanci da rashawa, amma a wannan lokacin babu wannan matsalar," ya ce.

Hotuna daga Grace Ekpu ta BBC