Sheikh Giro Argungu ya nemi afuwar 'yan Najeriya kan tsine wa "makiyan" Buhari

Sheikh Giro Argungu ya nemi afuwar 'yan Najeriya kan tsine wa "makiyan" Buhari

Latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron hirar BBC Hausa da Sheikh Argungu:

Daya daga cikin Malaman Izala a Najeriya Shiek Abubakar Giro Argungu ya nemi afuwar 'yan Najeriya a kan wani bidiyo da yake nuna malamin yana kakkausan kalamai a kan "makiya" Shugaban kasar Muhammadu Buhari.

Malamin ya shaida wa Nasidi Adamu Yahaya cewa bidiyon an nade shi ne tun a 2015 kuma ya yi kalaman ne sakamakon wata matsala da ta faru a siyasar wancan lokaci.

Bidiyon dai ya nuna malamin addinin yana kwashe wa marasa goyon bayan Buhari albarka sa'annan ya yi wa marasa son ci gaban Najeriya fatan hatsarin mota.

Sheik Abubakar ya ce ya yi nadamar yin wadannan kalamai kuma ya amince da kuskurensa.

Malamin ya ce a wancan lokaci ya yi raddi ne ga wata kabila mai suna 'yan tatsine.

Tun bayan da guguwar siyasar 2019 ta fara kadawa a Najeriyar aka samu rarrabuwar kai na malamai musamman na Izala a kasar.

A kwanakin baya an samu sabanin ra'ayi da Sheik Ahmed Gumi wanda daya daga cikin Malaman Izala ne a kasar.

Haka a wani bangaren an samu sabanin ra'ayi da Shiek Yusuf Sambo Rigachikun bayan ya bayyana ra'ayinsa na goyon bayan dan takarar jam'iyyar PDP Atiku Abubakar.