'Yan Ghana sun sako Najeriya a gaba da ba'a kan daga zabe

African child

Asalin hoton, Godong

'Yan kasar Ghana suna ta zolayar 'yan Najeriya tun bayan da hukumar zaben kasar INEC ta dage ranar zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki a makon da ya gabata.

'Yan Ghanar wadanda makwabtan Najeriya ne, sun yi ta nuna mamakinsu kan me 'yan Najeriya suka iya ne, "dama ba su iya girka dafa duka ba, shirya zabe ma sun kasa yi a tsare."

A yawancin lokuta dai 'yan Ghana da Najeriya kan tsokani juna ta hanyar musayar kalamai kan wasu abubuwan. Kamar dai yadda 'yan Ghana suka yi amfani da wannan damar ta baya-baya kan daga zaben Najeriya.

Wasu 'yan Ghanar sun yi ta tsokanar 'yan Najeriya a shafukan sada zumunta da muhawara da cewa bayan iya dafa teba da miyar shuwaka, sai me kuma 'yan Najeriya suka iya, tun da ko dafa dukar shinkafa mai dadi ba su iya ba.

Daga zaben da INEC ta yi dai ya kada su kansu 'yan Najeriyar, ta yadda suka kasa yarda da batun INEC din ganin cewa ta shafe shekara hudu tana shirya zaben amma kuma sa'o'i kadan gabanin a fara kada kuri'a ta sanar da dage shi.

Shugaban hukumar INEC, Mahmood Yakubu ya ce: "ba za a iya yin zaben a ranar da aka shirya ba."

Ya ce ya zama dole a dauki matakin don tabbatar da cewa an yi sahihin zabe.

INEC ta daga zaben ne zuwa Asabar 23 ga watan Fabrairu.