Daga zabe ya sa dala ta karye a Najeriya

  • Umar Shehu Elleman
  • BBC Hausa, Lagos
Kudin Amirya ya yi a kasuwar musayar kudadae ta 'yan chanji a Naijeriya
Bayanan hoto,

kudin kasar Amirka

Wasu rahotanni da ke fitowa daga Najeriya na cewa ana kara samun daloli na kudin Amurka suna yawo cikin kasuwar musayar kudade a jihohin Lagos da Kano da Kaduna da kuma Fatakwal.

Ana zargin cewa mafi yawa daga dalolin da ke yawo dai, na fitowa daga hannun 'yan siyasa da ke neman naira ne.

Tuni dai yawaitar dalar ta karya farashinta.

Bincike ya nuna a yanzu 'yan siyasa masu hannu da miya da ke da kudi, musamman wadanda suka tara daloli na kudin Amurka sun fantsama cikin kasuwannin masu musayar kudi inda suke neman naira ido rufe.

Kafin daga zaben dai ana sayen duk dala daya a kan naira 363, amma bayan dage zaben ta koma naira 356.

Ana zargin 'yan siyasa da neman nerar domin rarrabawa magoya bayansu da sauran 'yan siyasa da ke da fada a ji a lokacin kamfe ko kuma a lokacin gudanar da babban zabe na shugaban kasa a Najeriya.

Alhaji Nasiru Gulma fitaccen dan chanji ne da ke Legas, ya ce babu karya a game da yawaitar dalar Amurka a cikin kasuwar musayar kudaden, wani al'amari da hakan ya haifar da karya farashin dalar.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Wasu rahotanni na daban na cewa faduwar farashin dalar a Najeriya, ba za ta rasa nasaba da yadda 'yan kasuwar kasar China da sauran 'yan kasuwa suka tafi hutu tun bayan da gwamnati ta bayar da hutu domin gudanar da babban zabe ba.

To amma Alhaji Nasiru Gulma ya ce kawo wannan lokaci ana shaida shigowar dalar ta hannun 'yan siyasa.

Sai dai ya ce ba za a yi saurin zargin masu musayar kudi da suke da lasisi ba - illa dai sau da yawa hakan na faruwa daga hannun 'yan chanjin da ba su da lasisi.

Ba dai boyayyen al'amari ba ne cewa a shekara ta 2015, an wayi gari da aka samu karancin dala a bankuna da kuma ta yawaita a hannun 'yan Najeriya musanman 'yan kasuwa da sauran magoya bayan 'yan siyasa.

A bara, an ruwaito babban bankin Najeriya da yin wani gargadi cewa in har ba an dauki matakan da suka kamata a game da yadda 'yan siyasa suke sakin miliyoyin dalolin cikin kasuwar kasar ba, akwai yiwuwa ya shafi tattalin arzikin kasar da tashin farashin kayayyaki da hakan zai haifar da wani gibi a cikin tattalin arzikin kasar.

Hukumar EFCC mai yaki da ma su yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa dai ta danawa irin wadannan mutane da ake zargi da yawo da miliyoyi daloli da ke shigowa kasuwannin musayar kudi.

Wata majiya ta ce ko a makon jiya jami'an hukumar sun kai ziyara wasu daga cibiyoyin musayar kudi a jihar Legas, wanda suka gargade su da su kiyaye karbar kudaden kasashen waje a ba su tushensu ba.

Domin kuwa hakan zai iya haifar hukunci mai tsanani ya hau kan duk wanda aka kama.

Gwamnatin tarayya dai ta kayyade adadin kudin kasashen waje ga duk wani dan kasuwa zai rike ko yin hada-hadar kasuwanci a cikin kasar - wanda ko da kudin da yake bukata zai haura hakan sai ya samu sahalewar bankin da yake mu'amala shi.

Wannan dai wani mataki ne domin kaucewar yawan kudi a hannun jama'a da sakamakonsa zai zo da tashin farashin kayayyaki.