#ArewaMeToo: Abin da ya sa 'yan matan Najeriya suka fara magana kan cin zarafi

#ArewaMeToo: Abin da ya sa 'yan matan Najeriya suka fara magana kan cin zarafi

Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Wasu matasa mata a Najeriya sun yi gangami a shafin sada zumunta na Twitter, inda suka kirkiri maudu'in #ArewaMeToo wanda ya samu asali daga maudu'in #MeToo da ya yii tashe a shafukan sada zumunta a watannin da suka wuce.

Wannan gangami dai wani yunkuri ne na bai wa mata 'yan arewacin kasar muryar da damar fitowa su bayyana labaransu na cin zarafi ko fyade da maza ke masu.

Daya daga cikin wadanda suka kirkiri maudu'in a shafin Twitter, Fakhriyya Hashim ta ce labarin wata budurwa da ta fuskanci cin zarafi daga saurayinta shi ya zaburar da su.

Kuma ta ce maudu'in ya bai wa mata 'yan arewa da yawa damar fitowa su bayar da labarinsu a kafar Twitter kuma suna fatan wannan zai kawo babban sauyi a yadda ake kallon matan da aka ci zarafinsu a al'ummar Hausawa.

Bidiyo: Abdulbaki Aliyu Jari