Amurka ta taimaka wa Nijar da maganin malaria

Sauro ne ke haddasa cutar malaria

Asalin hoton, Getty Images

Gwamnatin Amurka ta taimaka wa jamhuriyar Nijar da magungunan zazzabin cizon sauro wato malaria na milyoyin CFA.

Tallafin dai ya hada da magungunan rigakafin zazzabin cizon sauro dama na magance cutar da zarar an kamu da ita.

Kazalika daga cikin tallafin da Amurkan ta ba wa Nijar, akwai gidajen sauro.

Amurka dai ta bayar da wannan taimako ne ga Nijar da zimmar rage yaduwar cutar ta malaria da akshi 50 cikin 100.

Wannan tallafi na Amurkan, na daga cikin wani tsari ne na kasar wajen tallafa wa kasashe masu tasowa.

Cutar zazzabin cizon sauro na daga cikin cututtukan da ke saurin kisan kananan yara da ma mata masu juna biyu a kasar.

Gwamnatin Nijar ta kasa yakin da take a kan yaduwar cutar zuwa gida uku da suka hada da neman tallafi da wadatar da al'ummar kasar da maganin rigakafin cutar da kuma tsaftace unguwanni.

Kasashen Afrika ne suka fi fama da cutar zazzabin cizon sauro, kuma yawancin wadanda ke mutuwa yara ne.