Shin Lawal Daura ya koma kan mukaminsa ne?

Lawal Daura

Asalin hoton, Twitter

Hukumar tsaron farin kaya a Najeriya, DSS, ta musanta rahotannin da ke cewa tsohon shugabanta, Lawal Daura, na jan akalar hukumar daga bayan fage.

A watan Agustan 2018 ne mukaddashin shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo, ya kori Lawal Daura daga shugabancin hukumar saboda kutsen da jami'an DSS suka yi a majalisar dokokin tarayyar kasar.

Osinbajo, wanda ya zama mukaddashin shugaban kasa lokacin da Shugaba Buhari ya tafi hutun kwana goma a Landan, ya nada Matthew B. Seiyefa a matsayin shugaban riko na hukumar.

Sai dai a watan Satumba, Shugaba Buhari ya nada Yusuf Magaji Bichi a matsayin shugaban hukumar ta DSS.

Wasu rahotanni da kafafen watsa labaran Najeriya suka bayar sun yi zargin cewa Lawal Daura na ci gaba da tafiyar da harkokin hukumar ta bayan fage.

Amma a sanarwar da mai magana da yawun hukumar, Peter Afunanya, ya aike wa manema labarai ranar Talata, ya musanta wannan zargi.

"An jawo hankalin hukumar DSS kan jita-jitar da ke cewa har yanzu tsohon shugabanta Alhaji Lawal Musa Daura yana tafiyar da harkokinta, da jimawa bayan an cire shi daga aiki.

"Muna so mu sanar cewa wannan labari karya ne, kuma muna gargadi ga duk wani mutum da ya yi hulda da shi cewa ya yi ne don kashin kasa."

Mai magana da yawun DSS ya kara da cewa hukumar ba za ta yarda da duk wani mutum da zai yi mata sojan-gona ba, don haka za ta hukunta duk wanda aka samu da yin hakan.