Waye ya fi amfana da dage zaben 2019?
- Daga Mayeni Jones
- Wakiliyar BBC News a Najeriya

Asalin hoton, AFP
Najeriya za ta gudanar da babban zabenta a ranar Asabar bayan dage zaben da aka yi lokacin wani taron manema labarai da shugaban hukumar ya jagoranta.
Dage zaben kwatsam a dare daya ya bai wa 'yan kasar mamaki kuma hakan ya kawo takura ga dubban 'yan Najeriyar musamman wadanda suka sha doguwar tafiya domin kada kuri'arsu.
Cibiyar masana'antu da kasuwanci ta Legas ta ce hakan ya jawo asarar dalar Amurka biliyan 1 da dubu dari biyar.
Hukumar zaben kasar ta kawo dalilai da dama da suka yi sanadiyyar dage zaben wadanda suka hada da zargin makarkashiya da aka yi musamman ta bangaren jigilar kayyayakin zaben da kuma matsalar yanayi da ya hana jirgin sama tashi domin kai takardun zabe.
Game da zaben 2019
- Mutum miliyan 84 suka yi rijistar zabe
- Kashi 51 cikin 100 na masu zabe suna kasa da shekara 35
- Akwai 'yan takarar shugaban kasa 73 da suka yi rijista
- Akwai rumfunan zabe dubu 120
Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriyar da kuma babbar jam'iyyar adawa ta PDP duk sun nuna rashin jin dadinsu dangane da dage zaben kuma jam'iyyun sun zargin junansu da kokarin tafka magudin zabe.
Akwai jam'iyyar da dage zaben zai fi zama alheri a gareta?
A sanarwar da aka fitar ranar dage zaben, jam'iyyar APC ta zargi PDP da kokarin dakushe kwarjinin dan takararta Muhammadu Buhari.
A dayan bangaren jam'iyyar PDP wacce dan takararta shi ne Atiku Abubakar ta zargi cewa hukumar zaben ta jinkirta zaben ne domin bayar da dama domin tafka magudin zabe.
Wata mai fashin baki a kan al'amuran yau da kullum Idayat Hassan da ke cibiyar dimokradiyya da ci gaba a Abuja ta bayyana cewa jinkirta zaben da mako guda ba zai yi wani tasiri wajen gudanar da magudin zabe.
Asalin hoton, Reuters
Ta kwatanta dage zaben da aka yi a yanzu da kuma na 2015 a lokacin mulkin PDP inda suka dage zaben da kusan mako shida saboda zargin da suke yi na hare-haren Boko Haram a arewa maso gabashin kasar.
Wancan dage zaben ta bayyana cewa ya zama alheri ga APC inda hakan ya jawo wa PDP bakin jini a matsayin jam'iyyar da ke neman mulki ko ta wane hali.
Amma ta nuna cewa dagen zaben zai iya zama alheri ga APC ma a wannan lokaci saboda za a iya samun karancin fitowar mutane, amma za a iya samun fitowar mutane da dama a wuraren da tun asali ana samun tururuwar fitowar mutane a ranar zabe,
Misali yankin arewa maso yamma da arewa maso gabas kuma nan ne Buhari ya fi yawan magoya baya.
Asalin hoton, AFP
Dagen zaben ya zama abin mamaki ga 'yan kasar
Wasu daga cikin masu fashin baki sun bayyana cewa dage zaben zai iya kawo cikas ga duka jam'iyyun sakamakon magoya bayansu da suka yi doguwar tafiya domin jefa kuria'a a makon da ya gabata ba za su iya wata tafiyar ba a wannan makon.
Wasu kuma sun ce dage zaben zai kawo matsala ga Shugaba Buhari sakamakon gazawar hukumar zaben da ta nuna ana alakantashi da shi.
Shugaba Buhari ne ya nada Shugaban Hukumar Zaben Mahmood Yakubu a shekarar 2015.
Shin zaben zai gudana a ranar Asabar?
Hukumar Zaben ta bayyana cewa ba za sake samun wani jinkiri ba, amma wasu masu sa ido a kan zaben suna nuna tantama a kan ko zaben zai yiwu a ranar 23 ga watan Fabrairu.
Tsohon Shugaban Botswana Festus Mogae ya shaida wa BBC cewa shi ma yana da tantama a kan ko an gama shirye-shiryen zaben.
Asalin hoton, AFP
Wasu magoya bayan Buhari a Abuja
Kuma Tsohuwar Mataimakiyar Shugaban Gambia Fatouma Tambajang ta ce itama tana da shakku a kan ko hukumar za ta iya gama shirye-shiryenta kafin zaben.
Ta ce yakamata a dubi abubuwa a zahiri musamman abubuwan da yakamata a ce an yi.
Asalin hoton, AFP
Yakin neman zaben Atiku a Adamawa
Da kuma shawo kan matsalar jigilar kayayyakin zaben, ta bayyana cewa yakamata a dawo da shaukin zaben da mutane suke dashi kafin dage zaben.
Me hukumar zaben ta ce?
Hukumar zaben ta ce tsaya wa a ranar da ta kara tsaidawa a matsayin sabuwar ranar zaben zai sa mutane su amince da su.
Kwamishan Hukumar na Abuja Alhaji Yahaya Bello ya shaida wa BBC cewa za a iya samun rikici idan ba a kawo kayan zabe a kan lokaci ba.
Ya ce ''mutane za su yi zaton cewa hukumar zaben ta boye su ne dagangan."
Asalin hoton, AFP
Cibiyar masana'antu da kasuwanci ta Legas ta jaddada amfanin kauce wa duk wani jinkiri, cibiyar ta yi gargadin cewa hada-hadar tattalin arzkiki ba za ta dawo yadda ya kamata ba har sai an gudanar da zabe a kasar.
Me zai faru a gaba?
Abu na farko da yakamata a fara yi shi ne kara bitar na'urorin tantance masu kada kur'ia wato Card Readers kusan guda dubu 280.
Ya kamata a kara sauya kwanan watan da ke kan na'urorirn zuwa sabon kwanan watan ranar zaben.
Asalin hoton, AFP
Yakamata a sauya kwanan watan da ke jikin na'urar tantance masu jefa kuri'ar
A wata sanarwa da hukumar zaben ta fitar, ta bayyana cewa wannan matakin zai dauki kusan kwanaki shida zuwa bakwai inda ake ganin cewa za a gama duba na'urorin a ranar Alhamis 21 ga watan Fabrairu.
Tuni aka mayar da muhimman kayyayakin zaben kamar su takardun zabe zuwa babban bankin Najeriya domin su zama cikin tsaro.
Ana sa ran rarraba su a kasar a ranar Juma'a 22 ga watan Fabrairu.
Malaman zabe da suka hada da na wucin gadin za su tafi a wannan rana.
Babu cikkaken bayani a kan abin da ya faru da malaman zaben da na wucin gadi da suka hada da dalibai masu yi wa kasar hidima wadanda tuni aka tura su a ranar Juma'a.
A dokar kasar, ana dakatar da yakin neman zabe sa'o'i 24 kafin zabe.
Bayan an rufe yakin neman zabe a wancan mako, a yanzu dai an bude kofa ga jam'iyyu su ci karensu ba babbaka.