Makafin da ke hawa Tsaunin Kilimanjaro

Trek participants at Mount Kilimanjaro

Asalin hoton, Paul Latham/Sightsavers

A ranar 20 ga watan Fabrairu, makafi bakwai da 'yan jagoransu hudu suka karasa tattakin da suka yi mai nisan mita 5,750 zuwa tsaunin Kilimanjaro a kasar Tanzania.

Masu tattakin sun shafe sa'o'i tara kafin hawa kololuwar tsaunin inda suka shafe mita 914.

A lokacin hawan nasu, sun ta fama da iska, da matsanancin sanyi, suna gab da isa ne suka hango wani jirgin sama yana wasa da fuffukensa inda yake sara masu a kan namijin kokarin da suka yi.

Asalin hoton, Paul Latham/Sightsavers

An kirkiro wannan tattakin ne domin nunawa duniya cewa makafi da ke Afirka ba wai sun gaza ba ne, ''idan aka horar da su suna da juriya da kwarin gwiwar gudanar da abubuwan birgewa.''

Asalin hoton, Paul Latham/Sightsavers

Mutum takwas ne suka fara wannan tattakin amma a daren 19 ga watan Fabrairu bayan sun sha wa wahalar hawa duwarwatsu sai suka yada zango a wani kogo, daga nan ne daya daga cikinsu ya fita daga cikin masu tattakin.

Asalin hoton, Paul Latham/Sightsavers

Geoffrey Salisbury na kungiyar makafi ta kasashen rainon Burtaniya ya ce ''a wannan ranar, mun sha fama da ciwon kafa kuma mutum biyu sun yi fama da rashin lafiya sakamakon jiri da suka sha bayan hawa wuri mai tsayi.''

''A karon farko mun tarar da ruwan kankara. Na hau saman kankarar, na fasa tsinin kankarar na kawowa John Opio mai fama da ciwon kai.''

''Tsananin sanyin kankarar ya tsoratar da shi har ya sa ya manta cewa ba shi da lafiya.''

''Ya hau da karfinsa amma daga baya ya sare sakamakon rashin cikakkiyar lafiyar ci gaba.''

Asalin hoton, Paul Latham/Sightsavers

An zabi wadanda suka yi tattakin ne daga daruruwan 'yan sa kai a Kenya da Uganda da Tanzania wadanda daga baya suka samu horo na mako biyu da ya hada da hawan igiya, yada sansani da dare da kuma lakantar sanin amfani da kayayyakin tsauni.

Asalin hoton, Paul Latham/Sightsavers

Asalin hoton, Paul Latham/Sightsavers

Asalin hoton, Paul Latham/Sightsavers

Jaridun Afirka a wannan lokacin sun ba da rahotanni a kan wannan tattaki kuma duka wadanda suka gudanar da tattakin an karbe su a matsayin jarumai.

Takalmansu uku da suka sude a yayin tattakin na nan an kafe su a gidan tarihin Uganda.