Daga Zaben 2019: Buhari ya roki 'yan Najeriya kada su kauracewa zabe

President Muhammadu Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya roki al'ummar kasar da su fito su kada kuri'a ranar Asabar 23 ga Fabrairun wannan shekarar.

A wani bidiyo da ya yi, Shugaban ya jajantawa 'yan Najeriya da suka yi tattaki zuwa mazabunsu don kada kuri'a amma Hukumar Zaben kasar, INEC ta sanar da sauya ranar zaben.

Ya yi kira ga 'yan Najeriya da kada su bari daga zaben ya sanyaya masu guiwa su ki fita zabe ranar Asabar.

Haka kuma, ya ce kada kuri'a hakkin 'yan Najeriya ne kuma kada su bari matakin da hukumar zaben ta dauka na daga zaben ya hana su bin hakkinsu.

Shugaba Muhammadu Buhari ya mika godiyarsa ga 'yan Najeriya bisa hakurin da ya ce sun nuna, kan matakin na INEC wanda ya ce zai bayar da daman gudanar da kyakkyawan zabe kuma zai tsarkake ayyukan zabe a kasar.

Hukumar zaben Najeriya, INEC dai ta dage zaben ne 'yan sa'o'i a fara kada kuri'a ranar 16 ga watan Fabrairu zuwa ranar 23 ga watan Fabrairu.

Shugaban hukumar, Farfesa Yakubu ya ce sun dauki matakin ne sakamakon matsalolin rashin kai kayan zabe a wasu yankunan kasar a kan lokaci.

A cewarsa, "Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya ta gana ranar Juma'a, 15 ga watan Fabrairu inda ta sake nazari kan shiriye-shiryenta na zaben shekarar 2019, don haka an dage zaben da za a yi ranar Asabar 16 ga watan Fabairu zuwa ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu. Kazalika, za a gudanar da zaben gwamnoni ranar tara ga watan Maris."

Dage zaben da INEC ta yi dai ya jawo cece-kuce a Najeriya da sauran kasashen duniya.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bacin ransa kan dage zaben haka shi ma babban abokin hamayyarsa Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP.

Wannan dai shi ne karo na uku a jere da ake dage zaben Najeriya bayan da hakan ta faru a shekarun 2011 da 2015 da kuma bana.

Karin labaran da za ku so ku karanta: