Za mu dauki matakin ba sani ba sabo a ranar zabe — Buratai

Babban hafsan sojin kasa na Najeriya Janar Tukur Buratai

Asalin hoton, @HQNigerianArmy

Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta yi umurni ga kwamandojinta su dauki mataki na ba sani ba sabo kan duk wanda ya nemi dagula sha'anin zabe a kasar.

Babban hafsan sojin kasa na Najeriya Janar Tukur Buratai ne ya bayar da umurnin a yayin da yake ganawa da manyan jami'ai da kwamandojin sojin kasar a ranar Laraba.

Ya ce satar akwati da kayayyakin zabe da aka saba yi a zabukan baya, laifuka ne da ke haifar da rikici da tashin hankali bayan zabe, don haka yanzu rundunar sojin kasar ta dauki mataki.

Tun da farko shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi gargadi ga barayin akwatin zabe inda ya umurci jami'an tsaron kasar daukar matakin ba sani ba sabo na rashin tausayi ga duk barawon akwatin zaben da suka kama.

A cikin jawabinsa, Janar Buratai ya bayyana irin rawar da sojoji za su taka a lokacin zaben 2019.

Ya ce wajibi ne a sake nazari tare da diba shirin da aka yi tun da farko kafin dage zaben shugaban kasa domin jaddada umurnin farko da aka ba sojoji.

"Duk wanda ya nemi sabawa dimokuradiyya za mu dauke shi matsayin makiyin Najeriya kuma za mu yi maganinsa," in ji shi.

Ya kara da cewa ganin yadda 'yan Najeriya suka nuna rashin jin dadinsu kan dage zaben Najeriya, ya zama babban kalubale ga sojoji da sauran jami'an tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya.

Ya ce za a janye duk wata tawagar soji da ke tare da 'yan siyasa, sannan ya umurci jami'an soji su nesanta kansu da sojojin da suka yi ritaya wadanda yanzu ke siyasa har zai an kammala zabe.

"Sojoji za su yi aiki tare da 'yan sanda wajen yin sintiri domin takaita zirga-zirga a ranar zabe, kuma za a gudanar da kwakkwaran bincike ga duk motocin da aka gani a hanya da kuma mutanen da aka kama da ke zargi," in ji Burutai.