Gobara ta hallaka mutum 78 a Birnin Dhaka na Bangladesh

Wata mata da ta rasa dan uwanta a gobarar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wata mata da ta rasa dan uwanta sanadiyyar gobarar

Jami'ai sun ce wata gobara mai ci kamar wutar daji na ci gaba da yin barna a wata gunduma da ke Birnin Dhaka mai tsohon tarihi na Bangladesh, inda mutum 78 suka mutu.

Gobarar ta tashi ne cikin dare a wani gida da aka ajiye wasu kayayyaki a kasan gidan, wadanda yawanci makamasan wuta ne.

Ana tsammanin wasu mutane da suka halarci wata liyafar aure na daga cikin wadanda suka mutu. Har yanzu ba asan abun da ya jawo tahsin gobarar ba.

Titunan gundumar Chawkbazar mai tsohon tarihi dai a tsuke suke kuma daf da juna.

Ana yawan samun tashin gobara a manyan gine-gine da ke yankunan da jama'a ke da yawa a Bangladesh, inda ake ganin rashin kula da bin tsari ke jawowa.

Daruruwan mutane ne suka mutu a shekarun baya-bayan nan.

A ranar Lahadi, gobara ta tashi a wata unguwar marasa galihu da ke birnin Chittagong na gabar teku har a kalla mutum tara suka mutu.

Shaidu: 'Mun ji wata kara'

Gobarar ta tashi ne a wani gini da misalin karfe 11.40 na dare agogon kasar a ranar Laraba, a yayin da mutanen yankin da dama ke barci.

Ta tashi ne a wani gini da ake ajiye sinadarai a kasan gidan, daga nan sai ta kama sauran gine-gine uku da ke kusa, kamar yadda jami'ai suka ce. Wutar ta rutsa da mutane da dama, wadanda suka kasa tserewa saboda turnukin hayaki.

Wadanda abun ya rutsa da su sun hada da mutanen da ke waje da baki da ke shagunan cin abinci da kuma wau mahalarta liyafar aure, kamar dai yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya fada. Yawancin gawarwakin dai sun kone ta yadda ba a iya shaida su.

Da yawa daga cikin wadanda suka ji raunin na cikin mummunan yanayi. Ana tunanin yawan wadanda suka mutu zai karu a yayin da ake ci gaba da neman mutane a gine-ginen da abun ya shafa.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Masu aikin ceto sun yi ta gano gawarwaki a ginin

'Yan kwana-kwana sun yi ta aiki fiye da sa'a biyar don kashe wutar, al'amarin da ya dinga gamuwa da cikas saboda matsatsin gidajen da rashin isasshen ruwan kashe wutar.

Wani mutum da shagonsa ya kone Haji Abdul Kader, ya ce ya ji wata babbar kara. Ya shaida wa AFP cewa: "Da na juya sai na ga gaba daya titin yana ci da wuta. Ta ko ina hayaki ne.

Firai Minista Sheikh Hasina ta bayyana kaduwarta kan wannan bala'i ta kuma mika sakon ta'aziyarta ga wadanda abun ya shafa, kamar yadda Jaridar Dhaka Tribune ta ruwaito.

'Bala'in da mutane ke ciki'

Daga Rakib Hasnet, BBC Bengali

Gundumar Chawkbazar na daya daga cikin muhimman wurare a tsohon Birnin Dhaka, wanda ya kafu tun shekara 400 da suka gabata a lokacin daular Mughal.

Waje ne da ake kasuwancin sinadarai da masana'antun turare duk da cewa hukumomi sun haramta ajiye sinadarai bayan wata mummunar gobara da aka yi a shekarar 2010.

Ana yawan ajiye babur mai kafa uku (Keke Napep) da kananan motoci a titunan wajen da rana. Hanyoyin wajen matsattsu ne ta yadda motocin bas ba sa iya wucewa.

Akwai wayoyin lantarki da na intanet sakale ta ko ina a saman gine-ginen, wadanda ke da matukar hatsari.

Amma ma fi munin abun shi ne yadda ake amfani da gidajen da mutane ke zaune ciki wajen mayar da su wajen sarrafa abubuwa, inda ake ajiye sindarai da tukunan gas a wajen.

Irin wannan bala'i da ya faru a baya

A watan Yunin 2010, wata gobara ta tashi a gundumar Nimtali inda mutum 124 suka mutu, wata gobara da ita ta fara daga wani gida da ake ajiye sinadarai.

Bayan wannan bala'i, wani kwamiti ya kawo shawarar cewa a daina ajiyar duk wani sinadari a gidajen da mutane ke zama, amma masu suka sun ce ba a dauki wani mataki na kwarai ba a shekarun baya-bayan nan.

A makon da ya gabata ne hukumomi suka sanar da wata fafutuka ta gano inda ake ajiye sinadarai ba bisa ka'ida ba a tsohon birnin Dhaka.

Asalin hoton, AFP

A shekarar 2013 ne aka gano rashin matakan kariya a lokacin da fiye da mutum 1,100 suka mutu, dubbai kuma suka jikkata a loakcin da wani gini na masana'antar tufafi ya rushe a Dhaka.