Daga Zabe: Ko gatan da gwamnati ta yi wa 'yan Najeriya zai sa su tafi kada kuri'a?

Asalin hoton, NurPhoto
Tun bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta daga zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki a makon da ya gabata, wasu 'yan kasar da dama sun bayyana cewa zai yi wahala su koma garuruwansu a wannan makon don yin zaben, bayan da suka je garuruwansu don yin zabe suka kuma dawo a makon da ya gabata.
Idan aka bincika sosai, za a ga cewa wadanda ke tsoron komawar na da dalilansu, ganin yadda mutane da dama suka yi rijistar zabe.
Kuma suna cewa sun kashe kudi sosai wajen yin bulaguron, kuma suna tunanin idan za su sake tafiyar, wani kudin za su sake kashewa.
Don karfafa wa masu kada kuri'a gwiwa su fito ranar Asabar, an yi shirin samar da wasu motoci kyauta da hutu da kuma muhalli wadanda gwamnati da wasu mutane suka dauki nauyin yin haka.
Gwamnatin Najeriya ta ba da hutu ranar Juma'a
Ministan Harkokin Gida Abdulrahman Dambazau wanda ya fitar da sanarwar, ya ce an ba da hutun ne don hakan zai taimaka wa masu kada kuri'a a zaben shugaban Najeriya da na 'yan majalisar dokoki.
'Yan kasar sun rika bayyana jin dadinsu bayan samun labarin:
An samar da motoci kyauta don zabe
Maudin #busesfordemocracy ya karade kafafen sada zumunta musamman a shafin Twitter.
A yankin arewacin Najeriya, kungiyar Katsinawa ta dauki nauyin samar da motoci kyauta daga Abuja zuwa Katsina, wato jihar da Shugaba Buhari ya fito.
Hakazalika akwai wani kamfanin sufurin jiragen sama ya yi rangwame ga farashin tikitin fasinjojinsa.
Wakilin sashen BBC Pidgin ya je ofishin kuma ya tabbatar da hakan. Sai dai har lokacin da ya bar ofishin jiragen bai yi tozali da wani da ya amfana da garabasar ba.
Biyan alabashin watan Fabrairu
A ranar Laraba ne gwamnatin tarayyar kasar ta ba da umarnin a biya albashin ma'aikata na watan Fabrairun ba tare da ba ta lokaci ba.
Ministan Yada Labarai Lai Mohammed ya ce an yi hakan ne don a saukaka wa ma'aikatan da za su yi tafiya don kada kuri'a a zabukan ranar Asabar.
Rage farashin man fetur
Kungiyar dillalan man fetur (IPMAN) ta bai wa mambobinta umarnin su rage farashin man fetur daga naira 145 zuwa naira 142 ko 140 a kan kowace lita.
Shugaban kungiyar Chindeu Okoronwo ya ce gudunmuwarsa ke nan ga ci gaban kasa.
"Mun dauki matakin ne don mu rage wa 'yan Najeriya wahalhalu a lokacin zabe. Mun yi hakan don karfafa wa jama'a gwiwa don su kada kuri'arsu.
"Saboda idan ka kada kuri'a ka sauke nauyinka a matsayin dan kasa," in ji shi.