Zaben 2019: Amsar tambayoyinku kan dokokin zabe a Najeriya

  • Mustapha Musa Kaita
  • Multimedia Journalist
Wane tanadi hukumar zabe tayi a kan idan masu zabe basu gama ba har lokaci ya wuce?

Asalin hoton, Getty Images

Wannan makala ce da muka yi bayan da muka bukaci ku aiko da tambayoyinku kan abin da kuke so ku sani dangane da dokokin zaben Najeriya.

BBC Hausa ta mika tambayoyin ga masanin shari'a Dakta Aminu Gamawa, da kuma Hukumar zaben kasar INEC domin amsa tambayoyin da wasu masu saurare da mabiyanmu suka aiko.

Za a iya zabe da katin zabe na wucin gadi?

Asalin hoton, Getty Images

Sanarwar da hukumar zabe ta kasa ta yi ita ce baza a bar mutumin da ke da katin zabe wanda ba na din-din-din ba ya yi zabe ba.

Na'urar tantance masu zabe ba za ta iya tantance katin zabe na wucin gadi ba.

Tuni dai hukumar zabe ta bayyana cewa kowa ya je ya karbi katin zabensa na din-din-din kafin rufe karba.

Wa ne hukunci ne ya hau kan wanda aka samu da katin zabe fiye da daya a rumfar zabe?

Ko wane dan kasa yana da 'yancin samun katin zabe guda daya idan ya kai shekaru 18.

Idan aka samu mutum da katin zabe biyu, ba za a ce kai tsaye ya yi laifi ba, wata kila ajiya ce amma sai a tsaya a duba sunansa ne duka a kai?

Idan sunansa ne duka a kai, hakan ya sabawa doka, domin sashi na 23 na dokar zabe ya haramtawa mutum mallakar katin zabe ta haramtaciyyar hanya.

Haka kuma kada kuri'a fiye da daya a zabe daya ya sabawa doka, idan aka samu mutum da wannan laifi, za a iya cin tararsa kudi da suka kai har naira dubu 500 ko kuma zaman shekara biyu a gidan yari.

Shin da tsoffin takardu ko sabbi za a yi amfani bayan dage zabe?

Tunda daga zaben aka yi ba a fara zaben ko aka soke ba, takardun da aka kawo na wancan zaben za a iya amfani da su.

Takardun da baza a iya amfani dasu ba sune wadanda suke da kamar kwanan wata, wadannan za a iya sauya wadansun su.

Kayayyakin zabe suna da muhimmanci sosai, shi yasa ma idan aka kai su jihohi ake kai su babban bankin Najeriya saboda muhimmancin su.

Shin ma'aikacin zabe zai iya zuwa cin abinci ya dawo ya ci gaba da aikinsa?

Asalin hoton, Getty Images

Ma'aikatan zabe 'yan adam ne kamar kowa, bukatar cin abinci ko zuwa makewayi za ta iya tasowa ko kuma tafiya sallah amma batun tafiya sallah bai wuce minti goma kuma akasari ba ma'aikaci daya ne a rumfar zabe ba wani zai iya tsayawa.

Babban abinda ake fadawa ma'aikatan zabe shine su tanadi ruwa da abincin da za su ci a rumfar zabe don kada ya zamana sun tafi cin abinci kuma wani abu ya faru.

Kuma bai kamata a ce 'yan siyasa ake jira za su dafa abinci su kawo ba saboda kada a ce ma'aikacin zabe yana goyon bayan wata jam'iyya.

Yakamata jama'ar gari su bada hadin kai ga jami'an zabe su gane cewa 'yan adam ne kamar kowa, amma kada kuma a ce ma'aikata gaba daya za su tafi makewayi su bar rumfar zabe ba kowa.

Akwai wani tanadi ga masu zabe idan lokaci ya wuce?

Asalin hoton, Getty Images

Tanadin da hukumar zabe ta kasa ta yi shi ne tabbatar da kawo kayan zabe a cikin lokaci da isowar ma'aikatan zabe kan lokaci.

Babban dalilin da ya sa ake samun matsalar, shi ne rashin kawo kayan zabe a kan lokaci ko kuma rashin isowar ma'aikata a kan lokaci kuma har da wannan dalili ne ya sa aka dage zaben ranar asabar.

Hakan ya zama wajibi ga jama'a su bayar da hadin kai su fito kan lokaci domin fara zabe.

Abin da doka ta ce shi ne idan aka rufe rumfar zabe, ba zai yiwu mutum ya ce a bude ma shi ya yi zabe ba, nauyi ne da ya rataya a kan mutane su fito a cikin lokaci su bi ka'ida su bi layi su yi abin da ya kamata su yi idan mutum ya kada kuri'arsa ya bar wurin saboda kada ya kawo rudani.

Shin ya dace jami'in tsaro ya karbi kyautar kudi a wajen jami'in jam'iyya?

Asalin hoton, Getty Images

Kuskure ne jami'in tsaro ko kuma ma'aikacin zabe ya karbi kudi daga wurin dan takara ko wata jam'iyya.

Dukkan jami'an tsaro da ake turawa ranar zabe domin samar da tsaro a ranar zabe gwamnati ce ke kula da su.

Bayan albashin da ake ba su akwai alawus-alawus da aka tanadar saboda aikin zaben da suke yi.

Saboda haka bai kamata su bi 'yan siyasa su karbi kudi ba ko su bari 'yan siyasa su raba masu kudi, hakan zai iya zubar masu da mutunci kuma hakan zai iya kawo tarzoma da tashin hankali.

Ya kamata jami'an tsaro da ma'aikatan zabe su guji karbar cin hanci, ko toshiyar baki hannun jam'iyyu ko wakilan jam'iyyu ko 'yan takara.

Shin wa ya dace ya zama jagoran makafi wajen dangwala kuri'a?

Asalin hoton, Getty Images

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

An yi tanadin yadda makafi za su kada kuri'a ta hanyar samar da takardarsu ta zabe ta daban da kuma abin da suka saba rubutu da shi da ake kira 'braile' a turance.

Za su dorar braile din ne a takardar zabe, kuma an samar da ita ta yadda za su iya shafa wa su gano jam'iyyar da za su dangwala wa.

Ga masu lalurar makanta da ba su yi karatu ba, hukumar INEC ta ce za su iya zuwa da jagora daga gida a wajen zabe.

Hukumar ta ce ba a yadda daya daga cikin jami'anta a rumfar zabe ba su yi wa mai lalurar makanta jagora ba.

An kuma yi tanadin wani babban gilashi a rumfar zabe ga zabaya masu lalurar gani, wadanda idan rana ta yi sosai ba su iya gani ba. Don haka an yi tanadin gilashin da zai kara girman bakaken jam'iyun siyasa.

Ya kamata a ba masu bukata ta musamman irin makafi da guragu kulawa a ranar zaben saboda wasu ba su iya zama cikin rana ko bin dogon layi.

Akwai tsofaffi da zabaya da mata masu ciki, irin wadannan ya kamata a ce mun yi dattaku mun ba su dama sun jefa kuri'a sun koma gida.

Karfe nawa baturen zabe zai aika da sakamako daga rumfar zabe?

Asalin hoton, Getty Images

Da zaran an gama zabe abin da ake so shi ne a kirga kuri'u a san yawan kuri'un duka 'yan takara suka samu.

Bayan haka akwai takardar da za a rubuta sakamakon zaben da aka gudanar, sai wakilan jam'iyyu su sa hannu sai kuma malamin zaben ya bayyana sakamakon zaben a wannan mataki sannan sai a turawa wanda zai tattara sakamakon ya aika.

A takaice babu wani takaimaman lokaci da aka bada domin aikawa da sakamakon zabe.

Abin da aka ce sh ine ana gama zabe bai kamata a yi jinkiri ba saboda jinkirin shi ke bayar da dama ga 'yan siyasa ko 'yan takara su sauya sakamakon zabe.

Tsawon wane lokaci za a fadi sakamakon zaben shugaban kasa?

Asalin hoton, Getty Images

Wannan ya danganta da yawan 'yan takara da masu jefa kuri'a.

A zaben shugaban kasa akwai 'yan takara 73, sannan akwai masu zabe wadanda suka yi rajista mutum miliyan 84.

A baya a zabukan da aka yi na shugaban kasa a cikin kwanaki uku ake bayyana sakamako, wato daga Asabar zuwa Litinin.

A wannan karon ma ana iya samun sakamakon ko ya haura zuwa Talata, inda a nan ne ake sa ran za a samu sakamako daga hukumar zabe kuma ita kadai ce ta ke da hurumin bayyana sakamako.

Dalilin da ya sa ba a gaggawar bayyana sakamakon zabe, sai an tattara sakamakon daga jihohi 36 a kasar da kuma birnin tarayya Abuja.