Da gaske dalolin jabu sun bazu a Najeriya?

Jami'an hukumar EFCC

Asalin hoton, Getty Images

Hukumar EFCC da ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ta yi gargadin cewa akwai dalolin jabu da ke yawo a kasar.

Sanarwar da hukumar ta aike wa BBC, ta ce ta fitar da gargadin ne bayan bayanan sirri da ta samu yayin da ake shirin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar tarayya.

EFCC ta yi kira ga 'yan canji su yi taka-tsantsan.

Sai dai kuma BBC ta tuntubi 'yan canji a Lagos da Abuja inda suka ce ba su taba cin karo da jabun dala masu yawan yadda EFCC ta ce ba a kasuwa, a 'yan kawanakin nan.

Sun ce dalar ce ma ta yi yawa a kasuwa, ana neman Naira tun makwanni biyu da suka gabata da ake shirin zaben shugaban kasa.

Amma sanarwar da EFCC ta fitar ta ce akwai dalolin da suka yi kama da na kwarai amma kuma binciken hukumar ya tabbatar da jabu ne.

Hukumar ta bukaci 'yan canji su sa ido sosai har zuwa a kammala zabe.

Wasu masharhanta dai na ganin EFCC ta fitar da sanarwar ne da nufin kara karya dala musamman zargin da ake cewa an samu yawaitar dalolin ne a kasuwa saboda yakin neman zaben dan takarar jam'iyyar adawa ta PDP Alhaji Atiku Abubakar.