Gidajen Burodi a Mali

Da zarar rana ta fito a Bamako, Mali, motocin bas da masu talla da kura ke cika tituna. Amma kafin nan, a lokacin da 'yan tsitrarun mutane ke dawowa daga masallaci inda suka yi sallar asuba, ana iya ganin babura dauke da burodi irin wanda da yawa daga cikin mutanen za su ci don samun kuzari a ranar.

Buru Niouman Bakery in Bamako, Mali in the early morning hours of 5 February 2019.

Asalin hoton, Annie Risemberg

Bayanan hoto,

Gidan gasa burodi na Buru Niouman a Bamako, Mali

Mali na da ingantacciyar al'adar girke-girke, kuma 'yan Mali na cin abincinsu na gargajiya, amma burodin wanda ya samo asali daga Faransa- mai dan karfi daga waje da lallausan ciki- ya zama abincin gargajiya a nan.

Ana yin burodin da filawa da gishiri da ruwa da yis kuma shi ne burodin da aka fi samu a gidajen burodi a Bamako, duk da cewa ana yi masu kwalliya da hotunan wani nau'in burodi mai kanannado.

Asalin hoton, Annie Risemberg

Bayanan hoto,

Ana yayyanka kwabin burodi zuwa kananan curi wanda za su zama sinkin burodi

Asalin hoton, Annie Risemberg

Bayanan hoto,

Wasu ma'aikata na bude jerin danyen burodi don gasawa.

'Yan Mali da yawa ba sa sayen burodi daga gidajen gasa burodin sai dai daga kananan shaguna.

Direbobin da ke rarraba burodin ga shaguna na fara aiki ne daga karfe 4 na asuba, su kuwa ma'aikatan gidajen burodin na fara nasu aikin kafin karfe hudu.

Su kan fara kwaba burodin ne da tsakar dare.

Ana sayar da burodi da yawa ga shaguna da gidajen abinci har ma da gidajen biki.

Manajan Buru Niouman, Youssef Sogoba, ya yi baynain cewa gidan burodin na sayen baburan da ke rarraba burodin kowace safiya, dauke da daruruwan burodi.

"Duk lokacin da yawan burodin da ka raba ya kai 50,000, babur din ya zama naka," a cewarsa.

Asalin hoton, Annie Risemberg

Bayanan hoto,

Wasu maza na shirya baburansu don tafiya rarraba burodi.

Asalin hoton, Annie Risemberg

Bayanan hoto,

Alhassan Djitteye, wanda ya kwashe tsawon shekara 10 yana aikin raba burodi, yana shirya burodi a kan wani akwati da ke makale da babur din sa

A cikin gidajen burodi, maza na tashi daga baccin rana da suka yi a kan tabarmi yayin da burodin ke kumbura, mataki na karshe kafin a sa burodin a cikin manya Injin gashi da kuma rarrabawa.

Asalin hoton, Annie Risemberg

Bayanan hoto,

Kalilou Sow na fitar da sabon burodin da aka gama gasawa a gidan burodin Guema Coura

Asalin hoton, Annie Risemberg

Bayanan hoto,

Wasu suna shirya burodi kafin a rarraba

Ana sayar da burodi guda mai tsawon mita 1 kan kudin sefa 250, kuma a kan gasa burodi 2,500 a rana.

Duk da cewa burodi ba abincin gargajiya bane a Mali, 'yan Mali da yawa na cin burodi da kwai don karin kumallo.

Asalin hoton, Annie Risemberg

Duka hotuna daga Annie Risemberg