Dangantakar Rasha da Amurka ta kara tsami

Michael Calvey

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Dan kasuwa Michael Calvey

Masu shigar da kara a Rasha na tuhumar wani dan kasuwar Amurka Michael Calvey da laifin zamba - lamarin da ya kara matsa wa dangantakar kasashen biyu da ke kara tabarbarewa.

Mista Clavey shi ne mai kamfanin zuba jari na Baring Vostok Investment Fund, kuma ama tuhumarsa ne da zambatar wani bankin Rasha mai suna Vostochny dala miliyan 38.

Ofishin jakadancin Amurka a Moscow ya ce Rasha ta hana su da iaylan Mista Calvey ganinsa kwana bakwai bayan da aka tsare shi.

A karkashin dokokin kasa da kasa, tilas Rasha ta bari jami'an ofishin jakadancin Amurka su gana da shi cikinkwana hudu da tsare shi.

Mista Calvey ya ce tuhumar da ake masa ba komai ba ne face rikicin kasuwanci tsakanin masu rike hannayen jarin bankin Vostochny, kuma ya musanta aikata wani laifi.

Hukumomin Rasha dai na rike da Mista Calvey ne tare da wasu mutum biyar.

A cikin Rasha kuma, wasu manyan 'yan kasuwa sun soki matakin tsare Ba'Amurken, inda suka ce matakin na iya sanyaya gwuiwar masu zuba jari a kasar.

Ko a ranar Alhamis, Ministan harkokin waje na Rasha Sergei Lavrov ya yarda cewa tsare Mista Calvey na da sarkakiya ta siyasa.

Dangantaka tsakanin Rasha da Amurka na kara tabarbarewa tun bayan da dakarun Rashar suka kwace yankin Crimea na kasar Ukraine a 2014.