Shin Afirka ta ci baya ne bin tafarkin Dimokradiyya?

  • Daga Dickens Olewe
  • BBC News
Zaben da aka gudanar a Congo a 'yan kwanakin nan ya sha suka daban-daban

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Zaben da aka gudanar a Congo a 'yan kwanakin nan ya sha suka daban-daban

Ana ta gudanar da zabbubuka a fadin nahiyar Afirka amma masana sun bayyana wasu zabukan a matsayin wadanda ba inganttatu ba ko kuma ba a gudanar da su a kan ka'ida ba.

Bincike ya nuna cewa akasarin 'yan Afirka suna son dimokradiya, amma wasu da dama kuma suna so a kauce wa wannan tsari zuwa wanda ya fi shi, wasu kuma mulkin kama karya kamar yadda wakilin BBC Dickens Olewe ya ce.

A shekaru uku da suka gabata, kasashen Afirka sun ce akwai raguwa da aka samu a ingancin siyasa da kuma bin doka kamar yadda masana suka bayyana.

A yanzu akwai kasashe 15 masu dimokradiya mai tangarda, sa'annan akwai 16 masu mulkin kama karya a nahiyar Afirka kamar yadda wani farfesan dimokradiya na jami'ar Birmingham ya bayyana bayan wani dogon nazari da ya yi na shekaru uku da suka gabata.

A ranar Asabar ne ake sa ran Najeriya za ta gudanar da zabenta da aka dage kuma tana daga cikin kasashen da aka lissafo a jerin gwanon kasashe masu tangarda da dimokradiyyar su.

Duk da wannan kalubalen, a kalla kashi 68 cikin 100 na 'yan nahiyar Afirka sun fi so su zauna a cikin al'ummar da za su wala ba, tare da wata takura ba, kamar yadda wani bincike na cibiyar ''Afrobarometer'' da aka gudanar a kasashe 34 ya ce.

Amma alkalumman sun ragu kadan da kusan kashi 72 cikin 100 a shekarar 2012.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Mawakin Mali Salif Keita

Shugaban shirin Afrobaromter Emmanuel Gyimah-Boadi ya ce '' 'yan nahiyar Afirka suna son cin ribar dimokradiyya.''

''Suna son a rage cin hanci da rashawa da kuma gudanar da ayyuka bisa gaskiya, sai gudanar da hukunci da kuma habbaka tattalin arziki.''

Wani mawaki a kasar Mali Salif Keita tuni ya cire rai da dimokradiya a Afirka. Inda ya bayyana cewa ''nahiyar na bukatar Shugaban mulkin kama karya mai tausayi kamar China.''

Ya ce ''kafin a samu dimokradiyya, ya kamata mutane su fahimce ta, kuma ta yaya mutane za su fahimta bayan kashi 85 cikin 100 na mutanen ba su iya karatu da rubutu ba?''

Yadda dimokradiyya ke sauya Afirka

A shekarar 1991, kasashen Benin da Zambia suka zama kasashe na farko masu tsarin jam'iyyar siyasa daya inda suka yi zabe da tsarin jam'iyyu da dama a Afirka.

Wannan zaben jam'iyyun adawa ne suka lashe zaben a kasashen.

Wannan ne ya zamo matakin ci gaba a dimokradiyya a nahiyar bayan an kammala yakin cacar-baka.

Kusan bayan shekaru 30 kenan, kasar wace ke yammacin Afirka tana daga cikin kasashe tara cikin 54 da ke nahiyar da aka yi itifakin suna da cikakken 'yanci sai kuma Zambia tana da 'yanci, amma ba wai cikakke ba kamar na sauran kasashen kamar yadda wani rahoto na ''2019 Freedom report'' ya bayyana.

Asalin hoton, Getty Images

Yawan kasashen da suke da cikakken 'yanci bai sauya ba tun bayan shekara goma.

Kasashe takwas da suka hada da da Senegal da Ghana sai Benin da kuma Namibia sai Botswana da South Africa da Lesotho sai Mauritius suna nan a yadda suke, sai dai kasar Tunisia ta cike gurbin Mali wace a yanzu ba ta da cikkaken 'yanci kamar da.

Kasashen Angola da Ethiopia da aka lissafa a matsayin wadanda ba su da cikakken 'yanci sun yi wani motsi a 'yan kwanakin nan da ya ba da mamaki bayan sun samu sabbin shugabanni a kwanakin baya.

Kimiyya da harkar zabe

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Mika mulki bayan gudanar da zabe sahihi na daga cikin sharuddan tantance ko wata kasa na gudanar da dimokradiyya ko kuma koma bayan haka.

Wasu kasashe na amfani da kimiyya wajen kara inganta zabukansu, amma wasu bangarori wannan bai magance wasu matsaloli ba da ake fuskanta.

Nanjala Nyabola, mawallafiyar littafin ''Digital Democracy, Analogue Politics,'' ta shaida wa BBC cewa ''kasashe da dama a Afirka na son amfani da kimiyya wajen gudanar da zabe sahihi da kuma samun amincewar jama'a, amma hakan ba zai yiwu ba.''

Ta ba da misali da zaben Kenya na shekarar 2017, inda ta ce duk da cewa an yi amfani da na'urar tantance zanen yatsu domin tantance masu zabe, da kuma amfani da na'ura domin tura sakamako kai-tsaye, amma duk da haka masu zabe ba su amince da zaben yadda ya kamata ba.

Godwin Nurunga daga jami'ar Nairobi ya shaida wa BBC cewa ''wata matsala ita ce muna da kasashe da suke gudanar da zabe ta hallartaciyyar hanya amma mara inganci.''

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Kasashe da dama suna amfani da kimiyya domin samun sahihin zabe

Tsohon shugaban Congo Joseph Kabila ya sa ido a kan zaben da ya fi kowane rikici a nahiyar Afirka.

Wasu sun kira zaben da ''karshen magudi.''

Martin Fayulu, wanda shi ne ya zo na biyu a zaben har yanzu yana tantama a kan nasarar da Felix Tshikedi ya samu.

Ya shaida wa BBC cewa ''wannan juyin mulki ne.''

Ya ce yana da goyon bayan 'yan kungiyar darikar Katolika wace ta ce tana da masu sa ido a harkar zabe kusan dubu 40 ya kamata a ce ya ci zabe.

Tuni dai Mista Fayulu ya kai kara kungiyar hadin kan kasashen Afirka domin kafa wani kwamiti domin kara kidaya kuri'un da aka kada a ranar 30 ga watan Disambar bara ko kuma sake zaben nan da watanni shida.

''Ya kamata mu girmama abin da 'yan kasar Congo suke so, dole dimokradiyya ta zama daya a ko ina,'' in ji Mista Fayulu.