Za a hukunta duk dan sandan da aka gani da dan siyasa a ranar zabe

Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Abubakar Adam

Asalin hoton, @inecnigeria

Bayanan hoto,

'Yan sanda sun ce sun shirya wa zaben Najeriya.

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce za ta hukunta duk wani jami'inta da aka gani tare da dan siyasa da nufin ba shi tsaro a ranar zabe.

Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Abubakar Adamu ne ya fadi haka a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ACP Frank Mba ya fitar.

Sanarwar da ke bayani kan shirin da rundunar 'yan sanda ta yi a ranar zabe ta yi gargadi ga jami'anta su nesanta kansu da 'yan siyasa ko manyan mutane da suke gadi a ranar zabe kuma duk wanda aka gani za a kama shi kuma a hukunta shi.

Sufeto janar na 'yan sandan ya yi kira ga 'yan sanda su nuna kwarewa a aikinsu kuma su kasance masu kishin kasa ba tare da nuna wa wani bangare fifiko ba.

Sanarwar ta kuma ce Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya, ya bayar da umurni ga kwamishinoninsa su tsaurara matakan tsaro a dukkanin jihohin kasar 36 hadi da Abuja babban birnin tarayya tare da tabbatar da tsaro a dukkanin runfunan zabe a fadin kasar.

Sannan sanarwar ta yi kira ga 'yan siyasa su gargadi magoya bayansu su kasance masu bin doka da oda tare da guje wa duk wani abu da zai haifar da tashin hankali da saba dokar zabe har zuwa bayan kammala harakokin zaben.

Tuni dai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa jami'an tsaro za su dauki mataki mai tsauri kan duk wanda ya nemi dagula sha'anin zabe.