Mun yaba da shirin INEC na zaben Najeriya - ECOWAS

Tawagar ECOWAS

Asalin hoton, Reuters

Tawagar kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma Ecowas da ke sa ido a zaben Najeriya ta ce ta yaba da shirin hukumar zaben kasar na gudanar da zaben shugaban kasa.

Misalin karfe 8:00 na safiyar Asabar agogon Najeriya ake sa ran bude rumfunan babban zaben wanda aka dage tsawon mako daya saboda matsaloli da suka shafi raba kayan zabe a sassan kasar.

Cikin wata sanarwa, jagorar tawagar Ecowas tsohuwar shugabar Liberia Ellen Johnson-Sirleaf ta ce tun dage zaben kasar a makon da ya gabata sun sa ido sosai ga ayyukan hukumar zaben kasar musamman kalubalen da ta fuskanta na raba kayan zabe.

Ta ce ta yi farin cikin ganin yadda aka tunkari matsalar ta hanyar aiki tukuru don magance ta domin samar da yanayi mai inganci domin gudanar da babban zaben kasar.

Ta yi jinjina ga 'yan Najeriya kan yadda suka yi hakuri da kalubalen da suka fuskanta yayin da aka dage babban zaben sa'o'i a bude rumfunan zabe.

'Yan Najeriya za su kada kuri'a don zaben shugabannin da za su ja ragamar kasar a matakin shugaban kasa da 'yan majalisar dattawa da 'yan majalisar wakilai.

Ecowas ta yi kira ga 'yan Najeriya su ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da bin doka da oda har zuwa lokacin da aka sanar da sakamakon zaben.