'Yan sanda sun bayar da belin Abdulmumin Jibrin

Kwamishinan 'yan Sandan Kano

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce an karbi belin dan majalisar tarayya Abdulmumin Jibrin da ta kama kan zargin tayar da rikici.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ne DSP Haruna Abdullahi ne ya tabbatar wa da BBC inda ya ce wasu wakilan jam'iyyar APC ne suka karbe shi beli.

'Yan sanda sun kama dan majalisar ne da ke wakiltar Kiru da Babeji a Kano tare da wasu 'yan siyasa kan zargin haddasa tashin hankali yayin da ake shirye shiryen zaben shugaban kasa.

An zargi Abdulmimin da sauran 'yan siyasa da hanawa tawagar jam'iyyar adawa ta PDP wuce wa, dalilin da ya haifar tashin hankali da rasa rayuka.

Daga cikin wadanda 'yan sanda suka kama har da shugaban karamar hukumar Babeji.

Rundunar 'yan sandan ta ce za ta ci gaba da bincike bayan da ta ba da belin Hon. Abdulmumin Jibrin.