Zaben Najeriya: Za a yi ta ta kare tsakanin Buhari da Atiku

Buhari ya ce ya inganta rayuwar 'yan Najeriya amma Atiku ya ce 'yan kasar sun kara fadawa cikin matsanancin talauci.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Buhari ya ce ya inganta rayuwar 'yan Najeriya amma Atiku ya ce 'yan kasar sun kara fadawa cikin matsanancin talauci.

'Yan Najeriya sun fita kada kuri'a don zaben shugabannin da za su ja ragamar kasar a matakin shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki a ranar Asabar da safe.

Misalin karfe 8:00 na safiyar Asabar agogon Najeriya aka bude rumfunan babban zaben wanda aka dage tsawon mako daya saboda matsaloli da suka shafi raba kayan zabe a sassan kasar.

'Yan takara sama da 70 ne ke neman darewa kujerar shugaban kasa a zaben, amma Shugaba Muhammadu Buhari na APC mai shekara 76, da abokin hamayyarsa Atiku Abubakar na PDP, mai shekara 72 ne suka fi jan hankali a zaben.

Shugaba Buhari ya ce ya aza tubalin ci gaban kasar, amma Atiku Abubakar ya ce an samu koma-baya kan sha'anin tsaro da tattalin arziki da makamantasu a gwamnatin Buhari.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

'Yan takara sama da 70 ne ke neman darewa kujerar shugaban kasa

Duk wanda ya lashe zaben zai fuskanci kalubalen rashin harken lantarki da cin hanci da rashawa da mastalar rashin tsaro da kuma tabarbarewar tattalin arziki.

'Yan takara sama da 6300 neman kujerun majalisar dokoki ta kasa,

Za a zabi 'yan majalisar dattawa 109 da kuma 'yan majalisar wakilai 360.

Ana ganin zaben 2019, shi ne mafi girma a tarihin Afrika inda ake sa ran mutum miliyan 84 za su kada kuri'a a zaben na Najeriya kasa mafi girma a nahiyar Afirka.

Hukumar zaben kasar ta tabbatar wa 'yan Najeriya cewa ta shirya wa zaben bayan kalubalen da ta fuskanta na raba kayan zabe wanda ya tilasta ma ta dage zaben a ranar 16 ga Fabrairu.

Hare-hare

Sa'o'i biyu kafin bude rumfunan zabe ranar Asabar, al'ummar Maiduguri, babban birnin jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar sun ce sun ji fashewar bama-bamai da harbe-harben bindiga.

A wata sanarwa, 'yan sandan jihar sun ce babu wata barazana ga jama'a. "Jami'an tsaro ne suka yi harbe-harben domin tauna tsakuwa," in ji sanarwar.

Jihar Borno dai ta kasance cibiyar mayakan Boko Haram wadda ta yi shirin ganin ba a gudanar da zaben ba.

Kamfanin dillanci labarai na Reuters ya rawaito cewa wasu da ake kyautata zaton 'yan kungiyar ne sun kai hari garin Geidam, inda suka tilasta wa jama'ar garin ficewa daga garin.

Me ya sa aka dage zabe?

Sa'o'i biyar kafin bude rumfunan zabe ne dai a ranar Asabar ta 16 ga Fabrairu hukumar zaben Najeria ta sanar da dage zaben.

Hukumar ta bayar da dalilan da suka janyo dage zaben da suka hada da yunkurin yin magudi da rashin kai kayan aiki mazabu da kuma rashin kyawun yanayi.

Yanzu hukumar ta INEC ta ce ta shirya tsaf domin tafiyar da zaben.

Yadda zaben yake?

Duk dan takarar da ya samu kuri'un da suka fi yawa, idan dai har ya samu kaso 25 na kuri'un da aka kada a jihohi 24 daga jihohi 36 na kasar.

'Yan takara 73 ne suke neman kujerar shugabancin kasar amma fafatawar ta fi zafi tsakanin 'yan takarar jam'iyyu biyu.

Taken Jam'iyyar shugaba mai ci, Muhammadu Buhari shi ne 'Next Level' wato kai Najeriya zuwa matakin ci gaba.

Ita kuma jam'iyyar adawa ta PDP wadda tsohon mataimakin shugaban kasar, Alhaji Atiku Abubakar yake takara na da taken 'to get Nigeria working again', abin da ke nufin jam'iyyar za ta dawo wa najeriyar hayyacinta.

Atiku Abubakar ya kalubalanci Shugaba Buhari da lalata shekaru hudun da ya kwashe a kan karaga.

Dukkanin 'yan takarar guda biyu dai sun fito daga yankin arewacin kasar mai yawan musulmai. Kuma dukkanninsu sun wuce shekara 70 da haihuwa.

Matsalolin Najeriya

Najeriya ce dai kasa mafi girma a yawan jama'a da kuma yawan albarkatun man fetur. To sai dai rashawa da cin hanci da kuma gaza zuba rarar da ake samu daga sayar da man a kasuwar duniya ne ke tarnaki ga cigaban kasar.

A 2016, kasar ta samu komadar tattalin arziki. An kuma samu jan kafa kafin kasar ta samu ta farfado, al'amarin da ke nuni da cewa ba a samar da isassun ayyukan yi ga miliyoyin matasan kasar da ke neman aiki ba.

Za a iya cewa kaso daya bisa hudu na matasan kasar ba su da abun yi.

Alkaluman masu zabe

•Yan takarar shugaban kasa guda 73

•Masu katin zabe miliyan 73

•Kaso 51 da masu kati 'yan kasa da shekara 35

•Akwai rumfunan zabe dubu 120a fadin kasar.

.......

Shugaba Buhari ya ce ya murkushe kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin kasar, to sai dai har yanzu kungiyar na da karfi.

Sannan kuma ana ta yawan samun rikici tsakanin manoma da makiyaya a yankin arewa maso tsakiyar kasar.

Najeriya dai ta fuskanci mulkin soji har zuwa 1999, duk da cewa an samu gwamnatocin dimokradiyya wadanda ba su yi tsawon rai ba kafin nan.

A bana kasar ke cika shekara 20 da dawo wa turbar dimokradiyya.

A 2015 ne aka zabi shugaba Buhari, lokacin da kasar ta kafa tarihi, inda dan takarar jam'iyyar adawa ya kayar da shugaba mai ci.