Gimbiyar Saudiyya ta zama jakadiyar kasarta a Amurka

Saudi Princess Rima bint Bandar al-Saud at an October 2018 event

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Gimbiya Rima ta gaji mahaifinta Bandar bin Sultan al-Saud, wanda ya rike mukamin jakadan Saudiyya a Amurka tun daga shekarar 1983 zuwa 2005.

Saudiyya ta sanar da cewa Gimbiya Rima bint Bandar al-Saud ce za ta zama sabuwar jakadiyar kasar a Amurka - mace ta farko da aka taba bai wa mukamin jakadancin diflomasiyya a masarautar.

An bayyana ba ta mukamin ne a bainar jama'a ranar Asabar.

Gimbiya Rima ta yi mafi yawan rayuwarta ta kuruciya a birnin Washington na Amurka.

Ta samu wannan mukami ne a mawuyacin lokacin da Saudiyya ke kokarin kashe wutar ce-ce-ku-ce da sukar da take sha daga kasashen duniya kankisan dan jaridar nan Jamal Khashoggi.

Masarautar Saudiyya dai ta amince cewa kashe Khashoggi aka yi a ofishin jakadancinta na Santanbul da ke Saudiyya, baya ga musawar da ta yi tun farko da kuma bayar da mabanbantan bayanai masu rikitarwa.

Ta gaji mahaifinta

Gimbiya Rima za ta maya gurbin kanin Yarima mai jiran gado ne a wannan sabon mukami, wato Yarima Khalid bin Salman, wanda aka ba shi mukamin mataimakin minsitan tsaro.

Asalin hoton, Handout via Getty

Bayanan hoto,

An sanya wa Mr Trumpya ido sosai kan zargin da ake wa YAriman Saudiyya na hannu a kisan JAmal Khashoggi

Ta gaji mahaifinta Bandar bin Sultan al-Saud, wanda ya rike mukamin jakadan Saudiyya a Amurka tun daga shekarar 1983 zuwa 2005.

Saboda wannan mukami ne ma ta yi mafi yawan rayuwarta a Amurka.

Ta yi digiri a fannin Ilimin Gidajen Tarihi daga Jami'ar George Washington.

Tun bayan komawarta birnin Riyadh a 2005, Gimbiya Rima ta yi aiki a bangaren gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.

Ta rike mukaman kasuwanci da dama da suka hada da shugabar kamfanin Harvey Nichols Riyadh.

Gimbiyar ta yi suna wajen fafutukar kare hakkin mata, a kasar da ake yawan sukarta da rashin daidaiton jinsi.

A baya-bayan nan ta yi aiki a Hukumar Wasanni ta masarautar, da fatan mayar da hankali wajen ganin an sa mata cikin harkar wasanni da motsa jiki.

An kuma san ta da mayar da aiki tukuru wajen wayar da kai kan ciwon sankarar mama.