Zaben 2019: Wainar da ake toyawa a kafafen sada zumunta a Najeriya

social media icons

Asalin hoton, Getty Images

Ku san za a iya cewa kafafen sada zumunta sun dade ba su samu rubdugun jama'a ba irin wannan rana da 'yan Najeriya ke kada kuri'ar zaben shugaban kasa da 'yan majalisar dokoki.

Tun dai wayewar garin Asabar ne maudu'ai iri-iri suka yi ta cin kasuwa a kafar Twitter kuma kusan duk sa'a guda sai an sami wani sabon maudu'i.

Yanzu dai batun da yake tashe shi ne #NigeriaDecides2019 wanda yake cike da wallafe-wallafe na masu zabe daga sassa daban-daban na Najeriya.

Mutane kan aiko da hakikanin bayanan abubuwan da ke faruwa a rumfunan zabensu tun daga lokacin fara kada kuri'a har zuwa rufewa da kuma kidaya kuri'un da aka kada.

Kawo yanzu ma wasu wadanda suka jira aka kidaya kuri'un da suka kada sun fara wallafa sakamakon abun da aka samu a akwatin da suka kada, inda suke fallasa yawan kuri'un da wasu manyan 'yan siyasa suka samu a mazabunsu.

Maudu'i na biyu ma fi shahara shi ne #Okota wanda a cikinsa mutane ke ta tafka mahawara da wallafa hotuna dangane da yadda ake magudin zabe da sayen kuri'u da fasa rumfunar zabe da ma kisan jama'a, a unguwar Okota da ke birnin Lagos.

Asalin hoton, Twitter

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Wasu masu wallafe-wallafen sun zargin jami'an tsaro da satar kayan zabe da fasa rumfunan zabe da ma tursasa masu zabe a maudu'an #Rivers da #Aguda a jihar Rivers.

Wani maudu'i kuma da ya tayar da hankali sannan ya kunshi kalamai da wallafe-wallafen nuna kiyayya da barazana ga zaman tare shi ne maudu'in #Igbos.

A wannan maudu'i dai an ta musayar kalamai marasa dadi tsakanin 'yan kabilar Igbo da sauran kabilun Najeriya, inda wasu kabilun ma suke barazanar ganin sun kori 'yan kabilar Igbo daga garuruwansu musamman na yankin kudu maso yammacin Najeriya.

Jama'a da dama sun yi amfani da wadannan maudu'ai wajen fallasa abubuwan da suka wakana a mazabunsu.

Yayin da wasu ke ganin abubuwan da aka wallafa a wadannan maudu'ai ka iya taimaka wa hukumar zabe da jam'iyyun siyasa sanin abubuwan da ke faruwa a wuraren da idanunsu ba su kai kai ba, wasu kuwa na ganin irin wadannan wallafe-wallafe ka iya janyo rikici ne kawai da watsa labaran kanzon kurege.