Atiku ya sha kaye a rumfar zabensa

Bayanan bidiyo,

Yadda aka kidaya kuri'u a rumfar Atiku

Latsa hoton sama domin kallon yadda aka kidaya kuri'u a rumfar Atiku

Dan takarar jam'iyyar APC shugaba Muhammadu Buhari ya lashe zabe a rumfar babban abokin hammayarsa na PDP Atiku Abubakar.

Jam'iyyar APC ta samu kuri'a 186, yayin da PDP ta samu 167.

Atiku ya sha kaye ne a mazabarsa ta Ajiya mai lamba 02 inda ya kada kuri'ar a gundumar Gwadabawa da ke karamar hukumar Yola ta arewa a jihar Adamawa.

Malamin zaben da ya sanar da sakamakon ya kawai fadi cewa yawan kuri'un da APC ta samu da kuma yawan kuri'un da PDP ta samu ba tare da fadin jam'iyyar da ta lashe mazabar ba.

Sannan APC ce ta lashe kujerun 'yan majalisar dokoki a mazabar ta Atiku a Yola inda 'yan takarar PDP suka sha kaye kamar yadda kamfanin dillacin labaru na Najeriya NAN ya ruwaito.

Karin wasu labaran