Zaben 2019: Me kayar da Buhari a fadarsa yake nufi?

Kuri'un zaben shugaban kasa

Asalin hoton, Getty Images

Dan takarar jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya kada abokin hamayyarsa Shugaba Muhammadu Buhari na APC a daya daga cikin rumfunan fadar shugaban kasar.

Wakilin BBC a fadar Shugaban Najeriya Haruna Shehu Tangaza shi ne ya tabbatar da sakamakon inda ya ce PDP ta lashe rumfa mai lamba 022 yayin da kuma APC ta ci rumfa mai lamba 021, mazabun da ke cikin fadar shugaban kasa.

PDP ta samu kuri'u 525 a rumfa mai lamba 022, yayin da APC ta samu kuri'a 465.

A rumfa ta biyu kuma mai lamba 021, APC ta samu kuri'u ne 552, yayin da PDP ta samu 502.

Idan aka hade kuri'un rumfunan guda biyu, jam'iyyar PDP ce kan gaba da rinjayen kuri'u 10, inda APC ta samu 1017, PDP kuma 1027.

PDP ce ta lashe zaben dan majalisar dattawa a mazaba ta 021 da yawan kuri'a hudu inda ta samu 536, APC kuma ta samu 532

Wasu dai na ganin yadda shugaba Buhari ya fadi a daya daga cikin rumfar Villa ya nuna cewa wani bangare a fadarsa ba ya jin dadin gwamnatinsa.

'Yan Najeriya dai yanzu sun fara dakon sakamakon zaben shugaban kasa bayan rufe rumfunan zabe a mafi yawancin sassan kasar.

A yayin da aka soma kidayar kuri'u, akwai inda ba a kammala zaben ba saboda tsaikun kawo kayayyakin zabe da wuri da kuma tangandar na'ura da aka samu.

Shugaban hukumar zabe Farfesa Mahmood Yakubu ne zai bayyana wanda ya yi nasara a zaben na shugaban kasa a hukumance bayan kammala tattara sakamakon zaben daga jihohin Najeriya 36 hadi da Abuja.