Zaben 2019: Yemi Osinbajo ya sha kaye a rumfarsa

Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo

Asalin hoton, @ProfOsinbajo

Jam'iyyar PDP ta lashe zaben shugaban kasa a rumfar mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo.

Kazalika jam'iyyar ta PDP ta yi nasara a rumfar zaben dan takarar gwamnan Lagos na jam'iyyar APC, Babajide Sanwo-Olu.

Dan takarar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya samu yawan kuri'u 384, a rumfar dan takarar mataimakin shugaban kasar na jam'iyyar APC a Lagos.

Osinbajo da ke takara da shugaba Buhari a jam'iyyar APC, sun samu yawan kuri'u ne 197.

Asalin hoton, Twitter/@jidesanwoolu

Bayanan hoto,

Masu sharhi sun ce faduwar Osinbajo da Babajide Sanwo-Olu a akwatunansu abin kunya ne

Mataimakin shugaban kasar ya sha kaye ne duk da ya bi layi tare da jama'a domin kada kuri'arsa.

Tun da safe Osinbajo ya kada kuri'arsa a rumfarsa da ke Victoria Garden City a Lagos.

A akwatu mai lamba Ward 019 da ke mazabar Lateef Jakande/Femi Okunnu a unguwar Ikoyi inda Sanwo-Olu ya kada kuri'a, PDP ta samu 52, yayin da APC ta samu 48.

Mutane dai za su yi mamakin yadda mataimakin shugaban kasar ya gaza lashe rumfarsa ganin yadda ya bi gida-gida sako da lungu a yankin kudu maso yammaci yana yakin neman zabe.

Kazalika za su yi mamakin shan kayen da Sanwo-Olu ya yi a akwatunsa, ganin cewa shi ne dan takarar gwamnan Lagos a APC mai mulkin jihar.

Bayanan hoto,

Yadda Yemi Osinbajo ya bi layin zabe