Zaben 2019: Shin wa zai lashe Kano?

  • Awwal Ahmad Janyau
  • BBC Abuja
Birnin Kano

Asalin hoton, Getty Images

Kano na daya daga cikin manyan jihohin da ke da matukar tasiri a zaben shugaban kasa a Najeriya.

Yankin arewa maso yammacin Najeriya ne ke da yawan kuri'u fiye da sauran sassan Najeriya, inda mutum kusan sama da miliyan 70 ke da 'yancin kada kuri'a, kuma Kano ce kan gaba.

Ana ganin duk wanda ya yi mamaya a Kano zai iya lashe zaben shugaban kasa.

Dan takarar APC shugaba Buhari yana da dimbin magoya baya a Kano amma abokin hamayyarsa Atiku Abubakar na PDP zai iya wawurar kuri'u a jihar.

Kano ita ce jiha ta daya da ta fi yawan jama'a a arewacin Najeriya, kuma ta biyu bayan Lagos da ta fi yawan jama'a a fadin kasar.

Alkalummar hukumar zaben Najeriya INEC sun nuna cewa jihar Kano ce ta biyu bayan Legas wajen yawan masu rijista inda ta ke da mutum miliyan 5,457,747, sannan mutum 4,696,747 ne suka karbi katinsu zuwa yanzu.

A zaben 2015, Buhari ya samu kusan kashi 90 na kuri'un da aka kada a jihar Kano, amma a bana akwai alamun Atiku zai yagi wani kaso na kuri'un ganin yadda Atiku musulmi ne kuma dan arewa sabanin zaben 2015 da Buhari ya fafata da Jonathan kirista kuma wanda ya fito daga kudu.

Kuma ana ganin Atiku zai samu kuri'u da dama daga magoya bayan jagoran jam'iyyarsa ta adawa PDP a Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wanda ya aza dan takararsa don kayar da gwamna mai ci kuma tsohon mataimakinsa Abdullahi Umar Ganduje na jam'iyyar APC.

Asalin hoton, @Anas_Sukola

Kwankwaso wanda ya fice daga APC zuwa PDP yana da dimbin magoya baya da ke bin akidarsa ta Kwankwasiyya kuma ya yi wa Atiku alkawalin kawo ma sa Kano.

Sai dai masharhanta na ganin yana da wahala a iya kada Buhari a Kano saboda da dama da ke ra'ayin kwankwansiyya Buhari za su zaba maimakon dan takarar da jagoransu ke ra'ayi.

Amma duk da haka, wasu na ganin Buhari zai yi wahala ya samu irin yawan kuri'un da ya samu a Kano sabanin yadda ya yi mamaya a zaben 2015.

Zargin bidiyon karbar rashawa da ake yi wa gwamnan APC a Kano ya kara rage wa jam'iyyar Buhari farin jini wanda ke da'awar yaki da rashawa.

Kanawa da dama na ganin daga hannun Ganduje da Buhari ya yi a yakin neman zabensa a Kano, tamkar amincewa da shi ne duk da babban zargin rashawa akansa.

Asalin hoton, TWITTER/@DAWISU

Kuma wasu na ganin kamar shugaban ya kara mara wa cin hanci da rashawa baya ne, duk da ikirarin yaki da matsalar da gwamnatinsa ke ikirarin tana yi.

Ko da yake a baya Shugaba Buhari ya nuna tababa kan bidiyon da ke nuna Gwamna Ganduje na karbar rashawar dalolin Amurka inda ya ce bai san irin na'urar da aka yi amfani da ita wajen sarrafa bidiyon ba.

Wasu na ganin wannan na iya yin tasiri sosai a sakamakon zaben 2019 a Kano ga shugaban.