Amsar tambayoyinku kan tsarin cin zaben shugaban kasa a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Akwai ka'idoji da aka shata ga tsarin cin zaben shugaban kasa a Najeriya.
Yawan rinjayen kuri'a na da matukar muhimmaci ga samun nasarar zaben shugaban kasa a Najeriya, amma akwai wasu sharuda da dole sai dan takara ya cika kafin yin nasara.
Dole sai dan takara ya samu kashi daya cikin hudu na adadin kuri'un da aka kada a biyu bisa uku na jimillar jihohin da aka yi zabe.
Hakan na nufin sai dan takara ya samu daya cikin hudu na kuri'u a jihohi akalla 24 daga jihohi 36 na Najeriya hadi da Abuja kafin lashe zabe.
Dan takara na iya samun rinjayen kuri'u amma ya kasa cin zaben shugaban kasa saboda gaza cika sharuddan cin zaben.
Don haka lisafin yawan kuri'u ba shi ba ne cin zabe a Najeriya.
Matakan cin zabe a takaice
- Lashe rinjayen kuri'un da aka kada, ya zama shi ya fi kowa yawan kuri'u a cikin 'yan takarar da suka fafata a zaben shugaban kasa
- Sai dan takara ya samu daya bisa hudu na kuri'un da aka kada akalla a jihohi 24 daga cikin 36 da ake da su a Najeriya
- Idan babu wanda ya cika wadannan ka'idoji daga cikin 'yan takarar, wajibi ne hukumar zabe ta tsayar da ka'ida ta uku
- Za ta diba 'yan takara biyu da ke kan gaba da suka fi yawan kuri'u sai su yi zabe zagaye na biyu
- Duk wanda ya fi rinjayen kuri'u a zagaye na biyu tsakanin 'yan takara biyu da suka fi rinjaye a zagaye na farko to shi ne ya lashe zaben shugaban kasa.