Zaben Najeriya: Sojoji sun kashe 'yan bangar siyasa a Rivers

Sanarwar ta kara da cewa an kashe soja daya a arangamar da aka yi tsakaninsu da 'yan bangar siyasar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sanarwar ta kara da cewa an kashe soja daya a arangamar da aka yi tsakaninsu da 'yan bangar siyasar

Rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarunta sun kashe 'yan bangar siyasa a jihar Rivers da ke kudu maso kudancin kasar.

Sanarwar da mai magana da yawun rundunar Kanar Sagir Musa ya fitar ta ce an kashe 'yan bangar siyasar ne bayan sun kai farmaki kan dakarun sojojin da ke aikin tabbatar da tsaro lokacin zabukan ranar Asabar.

Ta kara da cewa an kashe soja daya a arangamar da aka yi tsakaninsu da 'yan bangar siyasar.

"Bayanan da hedikwatar sojojin Najeriya ta samu sun nuna cewa wasu 'yan bangar siyasa sun kai hari kan dakarun runduna ta shida da ke aikin wanzar da tsaro lokacin zaben 2019 a Abonnema, da ke karamar hukumar Akuku Toru a jihar Rivers.

"Maharan sun toshe babbar hanyar da ke garin inda suka yi wa dakarunmu kwanton-bauna suka bude musu wuta, kana suka yi yunkurin cire shingen da aka sanya. Dakarunmu sun yi musu raddi inda suka kashe 'yan bangar siyasa shida. Sai dai an kashe sojanmu mai mukamin laftana".

Kanar Sagir Musa ya kara da cewa kwarya-kwaryar binciken da suka gudanar ya nuna cewa wani mutum mai suna Roland Sekibo, - wanda shugaban karamar hukumar Akuku Toru ne da Omodo - babban jami'in tsaro na karamar hukumar da kuma Kenneth, wadanda suka gudu, su ne ke da alhakin tare sojojin.

Rundunar sojojin ta sha alwashin hukunta duk wanda ke da hannu a wannan hatsaniya.