Zaben 2019: Kun san dalilin kama Buba Galadima a Abuja?

Buba Galadima

Asalin hoton, Getty Images

An kama babban dan hamayyar nan na Shugaba Buhari kuma mai magana da yawun PDP Buba Galadima a Abuja ranar Lahadi, kamar yadda iyalansa suka shaida wa BBC.

Wani makusancinsa ya ce suna zargin jami'an tsaron farin kaya ne na DSS suka kama dan siyasar da rana jim kadan bayan ya fita daga gidansa.

Wani makusancin dan siyasa a kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugabacin Najeriya a jam'iyyar PDP da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce sun tura wakilansu zuwa ofishin DSS domin bincika dalilin kama Buba Galadima.

Sai dai har kawo yanzu babu wani bayani daga hukumar ta DSS kan zargin kama jigon a bangaren hamayya.

Amma a wani bidiyo da ba a tabbatar da sahihancinsa ba, an ga Buba Galadiman yana wasu zarge-zargen, tare da kiran magoya bayan jam'iyyarsa su fito su kasa su tsare su tabbatar an kiraga kuri'unsu.

A bidiyon Buba ya ce: "Jama'a ku yi hakuri karshen zalunci da fir'aunanci da kama karya ya kusa zuwa karshe.

"A yanzu haka akasarin sakamakon da muka fara samu sun nuna muna kan gaba nesa ba kusa ba. Muna kan gaba, don haka kar ku bari wani jami'in tsaro ko na zabe ko wani dan iska ya dauki akwatinku ya kona.

"Yanzu ne fa ya kamata a yi sadaukarwa an kasa an tsare an tabbatar da an kirga kuri'un nan daidai."

A ranar Asabar ne dai kuma Festus Keyamo da ke magana da yawun kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC Muhammmadu Buhari, ya yi kira da a kama Buba Galadima, bisa zargin yana shirin bayyana sakamakon zabe na boge.

Buba Galadima dai shi ne shugaban R-APC wani bangare da suka balle daga jam'iyyar APC.

Kuma yana cikin masu magana da yawun kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar da ke takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar PDP.