Muhimman abubuwa uku da suka faru a washegarin zabe?

  • Abdulbaki Jari
  • Digital Journalist
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, Mahmud Yakubu
Bayanan hoto,

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, Mahmud Yakubu

Zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar Asabar a Najeriya ya bar baya da kura.

'Yan Najeriya na dakon sakamakon zaben da suka kada kuri'unsu na shugaban kasa da majalisar dokoki tarayyar

Miliyoyin 'yan kasar sun kada kuri'unsu a zaben inda a halin yanzu ake tattara sakamakon kuri'un da aka kada.

Ga muhimman abubuwa guda uku da suka faru a washegarin ranar zaben 24 ga watan Fabrairun.

Kama Buba Galadima

Bayanan hoto,

Buba Galadima tsohon makusancin shugaban kasa Buhari ne amma a yanzu yana adawa da gwamnatinsa

A washegarin ranar zaber ne jami'an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kama jigo a jam'iyyar adawa ta PDP, Buba Galadima.

An kama Buba Galadima a Abuja ranar Lahadi, kamar yadda iyalansa suka shaida wa BBC.

Wani makusancin dan siyasan a kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugabacin Najeriya a jam'iyyar PDP da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce sun tura wakilansu zuwa ofishin DSS domin bincika dalilin kama Buba Galadima.

Babu wani bayani daga hukumar ta DSS kan zargin kama jigon a bangaren hamayya.

A ranar Asabar, Festus Keyamo da ke magana da yawun kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC Muhammmadu Buhari ya yi kira da a kama Buba Galadima, bisa zargin yana shirin bayyana sakamakon zabe na bogi.

Buba Galadima dai shi ne shugaban R-APC wani bangare da suka balle daga jam'iyyar APC.

Kuma yana cikin masu magana da yawun kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar da ke takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar PDP.

An dage tattara sakamakon zabe zuwa Litinin

Bayanan hoto,

Cibiyar tattara zabe dake a Kano

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa a Najeriya Mahmud Yakubu ya ce an dage tattara sakamakon zabe na kasa sai ranar litinin.

Ya ce za a ci gaba da tattara sakamakon a ranar Litinin 25 ga Fabrairu da misalin 11:00 na safe.

Wannan ya zo ne bayan da jama'a a ciki da wajen Najeriya suka halarci dakin tattara kuri'un na kasa da ke a babban birnin tarayyar kasar.

Idan za mu iya tunawa, hukumar zaben ta dage zaben kasar wanda ta shirya gudanarwa daga ranar 16 ga watan Fabrairu zuwa 23 ga wata sa'o'i kadan kafin a fara kada kuri'a.

An ci gaba da zabe har zuwa Lahadi

Bayanan hoto,

Ana ci gaba da zaben da ba a kammala ba a wasu sassan Najeriya

Sakamakon matsaloli da aka samu a wasu wurare a ranar, an ci gaba da zaben har zuwa ranar Lahadi.

Yanzu haka an kammala zabe a rumfar zabe ta Zawan A da ke jihar Filato a kasar.

Ana ganin wannan zai kawo jinkirin wajen tattarawa da kuma bayyana sakamakon zaben na shugaban kasa