Yakubu Dogara ya lashe kujerarsa a Bauchi

Yakubu Dogara

Asalin hoton, @YakubDogara

Kakakin majalisar wakilan Najeriya Yakubu Dogara ya lashe kujerarsa ta dan majalisar tarayya a jihar Bauchi.

Hukumar zabe ce ta tabbatar da Dogara a matsayin wanda ya lashe zaben dan majalisar tarayya da ke wakilatar Balewa da Bogoro.

Dogara na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 73,609, inda ya doke babban abokin hamayyarsa Dalhatu Kantana na APC wanda ya samu kuri'u 50,078.

Hakan dai na nufin Dogara wanda ya sauya sheka daga APC zuwa PDP kafin zabe zai sake dawo wa majalisar tarayya, kuma akwai alamun zai nemi kare kujerarsa ta kakakin majalisar wakilai.

Tun da farko Dogara ya yi korafi kan yadda ake kokarin kwace nasarar da ya samu bayan ya yi zargin cewa an ki bayyana sakamakon da ya tabbatar da cewa shi ne ya yi nasara, inda abokin hamayyarsa ya karyata ikirarin.

Ana ganin Majalisar wakilai za ta kunshi tsoffi da sabbin fuska, inda yana da wahala wasu daga cikin tsoffin 'yan majalisar su dawo.

Asalin hoton, @YakubDogara

Bayanan hoto,

Saraki ya sha kaye a Kwara