'Yan sandan Najeriya sun kama mutum 128 da suka aikata laifukan zabe

Sufeto Janar na 'yan Sandan Najeriya

Asalin hoton, @PoliceNG

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce tana tsare da mutum 128 da ta kama a ranar zaben shugaban kasa wadanda ta ke zargi da aikata laifukan zabe.

A cikin wasu jerin bayanai da ta wallafa a shafin Twitter, rundunar 'yan sandan ta Najeriya ta yi ikirarin samun nasarar tabbatar da tsaro a zaben shugaban kasa da aka gudanar a sassan kasar.

Sanarwar ta ce an samu nasara duk da an samu hasarar rayuka a wasu wurare.

Ta ce laifukan da mutanen da ta kama suka aikata sun hada da wadanda suka shafi kisa, da satar akwatin zabe da sayen kuri'u da sojan gona da dai sauransu.

Rundunar 'yan sandan ta kuma ce ta kama makamai 38 da abubuwa masu fashewa da dama.

Sanarwar ta kuma ce Sufeto Janar na 'yan sandan ya yi umurni ga kwamishinoninsa na jihohi su kara daukar matakan tabbatar tsaro bayan kammala zabe har zuwa bayan bayyana sakamako.

Rundunar 'yan sandan ta ce yanzu ta mayar da hankali tare da daukar matakai sosai a cibiyoyin tattara sakamako da kuma shirin ko-ta-kwana kan duk wani yunkuri na dagula aikin tattara sakamakon a fadin Najeriya.