Buhari ya lashe zabe a karamar hukumar Atiku

Atiku Abubakar

Asalin hoton, @atiku

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP mai hammaya Alhaji Atiku Abubakar ya sha kaye a karamar hukumarsa da ke jihar Adamawa.

Shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC ne ya samu rinjayen kuri'u a karamar hukumar Yola ta arewa.

Atiku ya samu kuri'u 27,789, yayin da kuma Buhari ya samu kuri'u 43,865, kamar yadda Dr. Oye babban jami'in da ke tattara sakamakon zaben shugaban kasar na karamar hukumar ya bayyana.

Atiku ya sha kaye tun a rumfar zabensa da ya kada kuri'a tare da iyalinsa.

Shugaba Buhari ne ya lashe zaben a rumfar ta babban abokin hammayarsa na PDP Atiku Abubakar.

Jam'iyyar APC ta samu kuri'a 186, yayin da PDP ta samu 167.

Bayanan hoto,

Sakamakon zaben rumfar Atiku ta Ajiya

Karin wasu labaran