Ban taba fafatawa a zaben da na sha wahala kamar bana ba —Abdulmumin Jibrin

Jibrin

Asalin hoton, Twitter/@AbdulAbmJ

Dan majalisar wakilan Najeriyar nan mai yawan janyo ce-ce-ku-ce, Abdulmumin Jibrin, ya ce bai taba fafatawa a zaben da ya sha wahala kamar na shekarar 2019 ba.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter domin nuna godiya ga Allah kan nasarar da ya samu ranar Lahadi, Abdulmumin Jibrin ya ce ba zai sake tsayawa takarar majalisar wakilai ba.

"An yi nasara duk da kalubalen da muka fuskanta... Ban taba fafatawa a zaben da na sha wahala kamar wannan ba. Na kusa durkushewa. Wannan shi ne fadan karshe mai matukar sosai rai domin kuwa ba zan sake tsayawa takarar majalisar tarayya ba."

Jibrin ya sake yin nasara a kujerar dan majalisar da ke wakilar Kiru/Bebeji ta jihar Kano a tarayya ne a karkashin jam'iyyar APC inda ya samu kuri'a 41,070 yayin da abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP, Ali Datti Yako ya samu kuri'a 40,412.

Wannan shi ne karo na uku da Abdulmumin Jibrin zai wakilci kananan hukumomin Kiru/Bebeji a majalisar tarayya.

Gabanin zaben, 'yan sanda sun kama shi saboda zargin haddasa rikici lokacin da 'yan jam'iyyar PDP karkashin jagorancin Sanata Rabi'u Kwankwaso suka je yakin neman zabe yankin lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Majalisar wakilan kasar karkashin jagorancin Yakubu Dogara ta taba dakatar da Abdulmumin Jibrin bayan ya fallasa cewa an yi cushe a kasafin kudin shearar 2016 lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a kasar.

A wancan lokacin, dan majalisar shi ne shugaban kwamitin na kasafin kud na majalisar wakilai.

Asalin hoton, Twitter/@AbdulAbmJ