Abin da ya sa ba mu amince da sakamakon zabe ba – PDP

atiku

Asalin hoton, Getty Images

Jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta sanar da cewa ba za ta iya kau da kai ga abin da ta kira hatsarin da demokradiyyar Najeriya ke daf da fadawa ba.

A wata sanarwa da shugaban jam'iyyar Prince Uche Secondus ya fitar, jam'iyyar ta ce sakamakon da ke hannunta daga jami'anta da ta tura sassan kasar sun ci karo da wanda hukumar zabe ta INEC take sanarwa ba.

Jam'iyyar ta ce ba ta amince da su ba.

Daga nan ta zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da jam'iyyarsa ta APC da hada baki da hukumar zabe ta kasa, INEC kamar yadda ta ce domin su karkatar da akalar siyasar kasar.

Ta yi kira ga 'yan Najeriya su yi watsi da sakamakon zabukan da kawo yanzu hukumar zaben ta bayyana.

Jam'iyyar ta PDP ta kuma zargi jam'iyyar APC da murde zabukan da aka yi ta hanyar bayar da cin hanci ga masu zabe, da kuma tursasa wa mutane su zabe ta.

Ta kuma ce APC ta yi amfani da jami'an tsaro na 'yan sanda da sojojin Najeriya har ma da jami'an tsaro na farin kaya DSS har da hukumar EFCC domin razana abokan adawarta.

Sannan jam'iyyar ta PDP ta zargi APC da kokarin dakile sakamakon zaben, kamar yadda ta ce, APC ta tura wasu manyan jami'an gwamntinta su karkatar da sakamakon.

Jam'iyyar ta PDP ta ce kama Injiniya Buba Galadima da ta ce gwamnatin Buhari ta yi ya nuna karara cewa Buhari ya kafe sai ya ci gaba da mulki ko da jama'ar kasar sun zabi wani jagoran na daban.

Ta kuma yi kira da a sake zaben, ba tare da bata lokaci ba.

Chief Uche Secondus ya tabbatar wa mabiya jam'iyyar cewa tana kan hanyar samun cikakkiyar nasara a wannan zaben.

PDP ta kuma yi kira ga kasashen duniya da su sa baki a cikin abin da ta kira kwacen da jam'iyyar APC ke son yi mata domin ceto Najeriya daga matsalolin da ke jiran 'yan kasar, idan ba a dauki mataki ba.