Ana yi wa 'yan kabilar Igbo barazana' a Lagos

'Yan kabilar Igbo a Lagos

'Yan kabilar Igbo na fuskantar barazana a Lagos inda wasu 'yan daba suka bukaci su kwashe kayansu su koma kasarsu.

'Yan daban na barazana ne ga 'yan kabilar ta Igbo mazauna Legas kan zargin da suke yi cewa sun ki zaben jam'iyyar APC da ke mulki a jihar.

Wakilin BBC a Lagos ya ce shagunan 'yan kabilar ta Igbo a Oshodi sun kasance a rufe saboda barazanar da suke fuskanta.

Ana zargin 'yan kabilar Igbo ne da zaben dan takarar jam'iyyar PDP Atiku Abubakar wanda ya zabo mataimakinsa daga kabilar Igbo.

Akwai dai 'yan kabilar Igbo da dama da suka mamaye kasuwanci a Lagos cibiyar kasuwancin Najeriya.

Kura ta lafa amma ana fargabar abin da zai iya faruwa ba nan gaba.

Yanzu haka 'yan sanda a jihar na kokarin shawo kan al'amarin.