Saraki ya taya mutumin da ya kayar da shi murna

Saraki

Asalin hoton, @BUKOLASARAKI

Shugaban Najalisar dattawan Najeriya Bukola Saraki ya yi fatan alheri ga mutumin da ya kayar da shi a zaben kujerar Sanata ta jihar Kwara.

Wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Yusuph Olaniyonu, ya fitar ya ce ya dauki matakin ne duk kuwa da cewa an tafka kura-kurai a zaben da aka kayar da shi.

"Ko da yake an gudanar da akasarin zaben cikin kwanciyar hankali amma akwai kura-kurai da dama wadanda suka hada da na na'urar tantance masu kada kuri'a wacce ba a yi amfani da ita ba a kashi 70 cikin 100 na mazabu.

Kazalika an samu rahotannin masu kada kuri'a sun yi zabe fiye da sau daya, sannan jami'anmu na PDP sun kawo mana irin wadannan korafe-korafe a duk fadin jihar nan.

Shugaban majalisar dattawan ya ce jam'iyyar PDP reshen jihar Kwara za ta dauki matsaya kan wadannan kura-kurai.

Saraki ya yi fatan cewa duk 'yan takarar da suka yi nasara a jihar Kwara za su gudanar da ayyukan ci gaban jihar.

"A matsayina na mutumin da ya fito daga gidan da ya gina ginshikin siyasa da ci gaban jiharmu da mutanenta, fata na shi ne al'umarmu za ta samu mai kyautata mata a ko da yaushe.

"Samun sabbin shugabanni zai bai wa al'uma damar kwatanta ayyukan da muka yi da wadanda za su shigo. Ba ni da makiya a cikin dukkan 'yan takarar da suka yi nasara. Su ma 'yan jihar Kwara ne."

Sakamakon wanda hukumar zabe ta sanar an tabbatar da Saraki ya fadi a dukkanin kananan hukumomi hudu da yake wakilta.

Dan takarar APC ne Ibrahim Oloriegbe ya kayar da Saraki a yankin Kwara ta tsakiya da ya kunshi kananan hukumomin Ilori ta yamma da Ilori ta Kudu da Ilori ta gabas da kuma Asa.

Bukola Saraki na jam'iyyar PDP wanda kuma ya jagoranci yakin neman zaben Atiku ya samu jimillar kuri'u 68,994 a dukkanin kananan hukumomi hudu da yake wakilta.

Ibrahim Oloriegbe na jam'iyyar APC kuma ya samu jimillar kuri'u 123,808 a dukkanin kananan hukumomi hudu na Kwara ta tsakiya, sakamakon da ya ba shi nasarar doke Saraki.

Asalin hoton, FACEBOOK/BUKOLA SARAKI