Zaben 2019: 'Yan Najeriya na fada a Twitter

Maudu'in #IAMNorth

Asalin hoton, Twitter

Bayanan hoto,

'Yan Najeriya da dama ne suka yi amfani da wannan hoton a Twitter

Yayin da ake ci gaba da bayyana sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a Najeriya, 'yan kasa na fafata wani abu da ya yi kama da fada a shafin Twitter.

Ana ganin wasu magoya bayan jam'iyyar PDP ne suka fara kai wa magoya bayan APC hari ta hanyar gaya masu bakaken maganganu bisa dalilin jefa wa Shugaba Muhammadu Buhari kuri'a da suka yi a karo na biyu.

A cikin kalaman da suka rika wallafa wa a Twitter, sun zargi 'yan Arewacin Najeriya da jahilci, suka kuma zargi "al'ummar Yarbawa da bauta," suka kuma "siffanta 'yan kabilar Igbo da zama wofintattu (Efulefu)."

A matsayin martani, 'yan Arewa sun fito kwansu da kwarkwatarsu suka fara ruwan sakonni ta hanyar amfani da maudu'in #IamNorth da ke nuna alfaharin kasancewarsu 'yan Arewa, ciki kuwa har da magoya bayan PDP din kansu.

Wasu sun yi amfani ne da maudu'in don bayyana abubuwan da suka shafi al'ada da kuma yin alfahari da ita:

Wasu kuwa sun yi kira da a sassauta kalamai domin zaman Najeriya kasa daya.