Zaben 2019: Har yanzu ba a san inda Buba Galadima yake ba

Buaba Galadima

Rahotanni na nuna cewa har yanzu ba a san inda mai magana da yawun kwamitin neman zaben Atiku Abubakar Buba Galadima yake ba.

A wata sanarwa da kafar yada labarai ta PR Nigeria ta aiko wa BBC, ta ce ta tuntubi hukumar tsaro ta farin kaya DSS da hukumar 'yan sanda da kuma sojoji sun kuma tabbatar da cewa Buba Galadima baya hannun jami'an tsaro tun bayan da aka dauke shi ranar Lahadi, kwana guda bayan zabukan kasar.

A ranar Lahadi ne iyalan Buba Galadima suka tabbatar wa da BBC cewa suna zargin jami'an tsaron farin kaya ne na DSS suka kama dan siyasar da rana jim kadan bayan ya fita daga gidansa.

Wani makusancin dan siyasa a kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugabacin Najeriya a jam'iyyar PDP da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce sun tura wakilansu zuwa ofishin DSS domin bincika dalilin kama Buba Galadima.

Masu magana da yawun hukumar DSS Peter Afunanya da na 'yan sanda Frank Mba da na soja Kanal Sagir Musa duk sun yi watsi da zargin cewa sun kama Buba.

Sai dai duk da wannan batu nasu har yanzu ba a san inda Buban yake ba kamar yadda iyalansa suka tabbatar.

Ana zargin dai an kama Buba ne saboda bullar bidiyo da ba a tabbatar da sahihancinsa ba, an ga Buba Galadiman yana wasu zarge-zargen, tare da kiran magoya bayan jam'iyyarsa su fito su kasa su tsare su tabbatar an kiraga kuri'unsu.

A bidiyon Buba ya ce: "Jama'a ku yi hakuri karshen zalunci da fir'aunanci da kama karya ya kusa zuwa karshe.

"A yanzu haka akasarin sakamakon da muka fara samu sun nuna muna kan gaba nesa ba kusa ba. Muna kan gaba, don haka kar ku bari wani jami'in tsaro ko na zabe ko wani dan iska ya dauki akwatinku ya kona.

"Yanzu ne fa ya kamata a yi sadaukarwa an kasa an tsare an tabbatar da an kirga kuri'un nan daidai."

A ranar Asabar ne dai kuma Festus Keyamo da ke magana da yawun kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC Muhammmadu Buhari, ya yi kira da a kama Buba Galadima, bisa zargin yana shirin bayyana sakamakon zabe na boge.

Buba Galadima dai shi ne shugaban R-APC wani bangare da suka balle daga jam'iyyar APC.

Kuma yana cikin masu magana da yawun kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar da ke takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar PDP.