Kalubalen da Shugaba Buhari zai tunkara bayan lashe zaben 2019

President Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto Getty Images

Shugaban Najeriya mai shekara 76, Muhammadu Buhari ya lashe zabe a karo na biyu, inda zai sake wani wa'adin mulki na shekaru hudu a karo na biyu.

Editan BBC na Afirka, Fergal Keane ya yi nazarin dimbin kalubalen da shugaban zai tunkara.

Wannan zaben ba za a taba ayyana shi a matsayin al'amarin da ke bayar da tabbacin bude babin sabuwar rayuwa ba.

Shugaba Buhari da abokin hamayyarsa wanda ya sha kaye, Atiku Abubakar, an dade ana damawa da su a harkokin siyasar Najeriya, tsawon shekaru.

Kuma jam'iyyu (masu karfin tasiri a kasar), ana yawan alakanta su da fifita 'yan uwa da abokan arziki (fiye da al'ummar kasa) da cin hanci da rashawa.

A gaskiya nasarar Buhari a wannan zaben ana iya dangantata da rashin yarda (ko kin amincewar da) al'umma suka yi da abokin hamayyarsa, al'amarin da ya zamar masa dole ya yi ta kokarin kare kansa daga zarge-zargen cin hanci da rashawa a lokacin yakin neman zabe.

Shugaban kasa ya yi wani dan yunkuri a wa'adin mulkinsa na farko, wajen shawo kan cin hanci da rashawa, al'amarin ya haifar wa kasar asarar biliyoyin kudi.

Amma shi a kashin kansa ba a taba samunsa (ko kama shida tuhumar almundahana ko badakalar satar kudin al'umma ba.

Sai dai an dade ana sukar lamirinsa kan rashin hanzarin aiwatar da ayyuka ko karade ko'ina da ko'ina cikin hanzari.

Shin abin tambaya a nan, ko zai kara yunkuri da kazar-kazar a wa'adin mulkinsa karo na biyu.

Hakikanin abin fahimta da ake bukata a rayuwa: al'amarin cin hanci da rashawa ya yi matukar kamari, lamarin da ya baibaye harkokin rayuwar al'umma.

Har ta kai ana bukatar natsuwa da kyau wajen tunkarar matsalar, tare da karfin hali da tabbtar da abin da ya dace, lamarin da ake ganin Shugaba Buhari ya rasa a wa'adin mulkinsa na farko.

Jinyar rashin lafiya da ya yi a wajen kasar, inda ya nemi magani a Landan kan wata cutar da ba a bayyana ba, na nuni da lakakin mulki fiye da zaburar tsayuwa tsayin daka.

Sai dai Shugaba Buhari ya yi sa'ar zabo mataimaki.

Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya fito da kansa a matsayin zakakuri lokacin da ya yi rikon kwarya, musamman yadda aka ga ya yi wajen tarairayar harkar tsaro da daidaita kimar darajar Naira (a harkokin hada-hadar kudi), lokacin da aka yi fama da matsanancin halin tattalin arziki.

Idan an yi nazarin yadda aka yi wa Buhari lakabin "Baba Go Slow - Mai tafiyar hawainiya." Ya dauki watanni shida kafin ya nada 'yan majalisar mulki a karo na farko.

Hakkin mallakar hoto Facebook/Nigeria Presidency
Image caption Wannan ne karo na biyu da Buhari yake lashe zabe

Matsala ta biyu da yake fama da ita wajen yaki da cin hanci da rashawa shi ne rashin managarcin goyon baya a siyasance.

Akwai tabbacin goyon bayan al'umma da Buhari ya samu, amma jam'iyyarsa ta yi sako-sako (wajen bin kadin laifukan) manyan 'ya'yanta da ake zargi da azurta kansu ta hanyar cin hanci da rashawa.

Fargabar da ake da ita a nan ita ce, kusan ko'ina barayin dukiyar al'umma za su ci gaba harkokinsu ba tare da an daga musu kara ba, kuma su kassara dabarun bunkasa tattalin arziki.

A fannin tattalin arziki kasar ta dogara ne kan kudin man fetur da kashi 70 cikin 100, ta inda gwamnati ke samun kudin shiga - wannan al'amari an shafe tsawon lokaci kan wannan turba har ta kai ga Najeriya ta afka cikin matsalar tattalin arziki a tsakanin shekarun 2016 zuwa 2017.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Magoya bayan Buhari sun kaure da murna a ofishin jam'iyyar APC a Abuja

Bankin Duniya ya yi hasashen rashin bunkasar tattalin arziki a shekara mai zuwa, inda aka kimanta bunkasar da kashi 2.2 cikin 100 a badi, bisa la'akari da yawan rashin aikin yi da ya kai kashi 20 cikin 100.

Kuma kimanin rabin al'ummar kasar na fama da matsanancin talauci. Don haka kawo karshe dogaro da man fetur wajen samun kudaden shiga akwai bukatar a hanzarta.

Sannan Shugaba Buhari na fuskantar dimbin matsalolin barazanar harkokin tsaro, tun daga kan karon-battar manoma da makiyaya a yankin tsakiya, samar da dorewar zaman lafiya a yankin Neja-Dalta.

Kuma abin damuwa mafi muni shi ne farfadowar masu tsaurin ra'ayin Musulunci a arewacin kasar.

Kuma Boko Haram reshen 'yan kungiyar tada kayar bayan Musulunci da ke Afirka ta Yamma, wadda a Ingilishi ake yi wa lakabin ISWAP, wadanda suka fake da lokacin zabuka suka kai muna nan hare-hare, wadanda suka hada da harba rokoki zuwa cikin kwaryar birnin Maiduguri a ranar zabe.

A wajen shugaban kasar da ya kai makurar karfin ikon mulkinsa wadannan al'amura da ke tunkararsa sun zame masa karfen-kafa a jerin kalubale.

Kuma ga shi Buhari yana cikin shekarunsa 70 da doriya, tattare da matsalolin rashin lafiya da ya yi fama da su.

Akwai yiwuwar nasarar da ya samu ta farfado da shi a wa'adin mulkinsa karo na biyu, wanda zai kasance mai karsashi fiye da na farko.

Ba don hadarin da ke tattare da kasancewar Najeriya rakumi da akala ba, tare da takaicin matasa wadanda su ne fiye da rabin yawan al'ummar kasar.

Matukar ana son al'umma ta aminta da tsarin dimokuradiyya ya samu dorewa, akwai bukatar ganin lallai mutanen da aka zaba a mukaman siyasa sun kawo wa al'umma dimbin alfanu.

Ta yiwu wannan ya dan bayar da hasken dalilin da ya sa aka samu karancin yawan wadanda suka fito kada kuri'a kasa da kashi 35 cilkin 100.

Idan an kwatanta da adadin wadanda suka fito zabe a shekarar 2015, wato kashi 44 cikin 100.

Wannan ita ce kididdigar alkaluman da suka dugunzuma damuwar daukacin jam'iyyun siyasa a Najeriya.